An Fallasa Yadda Ministar Kudi Ke Amfani Da Shaidar Tsallake Bautar Kasa (NYSC) Ta Bogi

 

Shin Buhari Zai Koreta?

Wani sabon rahoto da jaridar ” PREMIUM TIMES” ta wallafa ya tabbatar da cewa Ministar Kudi, Kemi Adeosun ba ta halarci shirin yiwa kasa hidima (NYSC) wanda ya zama wajibi ga duk wanda ya kammala karatun digiri kuma bai wuce shekaru 30 ba, ta yadda za a tura shi wata jiha na tsawon shekara guda.

A bisa tsarin na NYSC, idan mutum ya wuce Shekaru 30 a ya yin kammala karatunsa, za a ba shi shaidar tsallaka halartar shirin amma Rahoton ya nuna cewa, Ministar ta mallaki shaidar tsallake shirin ta bogi, duk da yake a lokacin da ta kammala karatunta a wata kwaleji da ke Ingila, tana da shekaru 22 da haihuwa.

Bayan ta kammala karatunta, Ministar ta yi ayyuka a kamfanoni da dama a kasar Ingila sannan bayan ta dawo gida Nijeriya, ta rike mukamin Kwamishiniyar Kudi na jihar Ogun. Dokokin shirin na NYSC ya tanadi hukuncin zaman gidan kurkuku na tsawon shekara guda ga duk wanda ya Tsallake shirin, alhali shekarunsa ba su zarce 30 ba kuma dokar shirin ya haramta bayar da aikin gwamnati ko na kamfani ga duk wanda bai halarci shirin ba.

Rahoton ya nuna cewa a lokacin da Shugaba Buhari ya tura sunar Ministar ga majalisar tarayya don tantance ta, shugabannin majalisar sun gano wannan matsalar amma kuma suka kawar da kai amma kuma a halin yanzu, majalisar na amfani da Ministar wajen samun haramtattun kudade daga asusun tarayya wanda ya hada da Naira Bilyan 10 da ta baiwa majalisar kwanan nan, don biyan kamfanonin da suka yiwa ‘yan majalisar kwangilar kawo masu motoci wanda hakan ya saba matsayin Shugaba Buhari.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *