Gwamnan Jigawa Ya Amince A Kashe Naira Bilyan 2 Domin Gina Asibitin Kwararru A Kazaure

 

Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori

Majalisar Zartawa Ta Jihar Jigawa, Karkashin Jagorancin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, Ta Amince A Kashe Zunzurutun Kudi Har Naira Biliyan Biyu, Domin Gina Sabon Asibitin Kwararru A Karamar Hukumar Kazaure.

Kwamishinan Watsa Labarai Na Jihar Jigawa Alh Bala Ibrahim Mamsa, Ne Ya Bayyana Haka Ga Manema Labarai Jim Kadan Da Kammala Zaman Majalisar Zartawa Jihar Jigawa, Wanda Aka yi Ranar Laraba A Fadar Gwamnatin Jihar Dake Birnin Dutse.

Kwamishinan Ya ce An Bada Aikin Ga ‘AFDIN Construction Limited’. Inda Aka Ba su Wa’adin Makwanni Sittin Domin Kammala Aikin.

Shugaban Karamar Hukumar Kazaure Alh Jameel Uwais Zaki Ya Bayyana Jin Dadinsa Gami Da Godiya Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Bisa Yadda Yake Aiyukan Alkairin A Karamar Hukumar Kazaure, Daga Karshe Shugaban Karamar Hukumar Kazaure, Yace Al’ummar Kazaure Zasu Baiwa Gwamna Badaru Abubakar, Kuri’u Fiye Da 2015

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *