BANA GOYAN BAYAN TSIGE PMB

 

Ra`ayin Sheik Badaru Kano

DA KOTU DA ‘YAN TSOHUWAR PDP BABU ABINDA SUKA ISA SU YI WA BUHARI SAI ABINDA ALLAH YA RUBUTA MASA

Ina Fatan Buhari Ya kai Bantansa a Zaben 2019 Saboda Mun ga Ya Debo Aiyukan Alkairi ga Yankinmu na Arewa Kamar Yashe Teku Zuwa Naija, Aikin Titi Daga Abuja Zuwa Kano Har ma Zuwa Maiduguri, Samar da Manyan Kamfanonin Taki da Shigo Da shi, da Farfado da Mutumcin Nijeriya a idon Duniya, Wannan Shine Abinda Muke Fata Kuma Aiki Ya Fara A Zahiri, Muna Kara Shawartarsa da Duk Wanda Ya Kasa Rike Aikinsa A cire shi A saka Wadanda Suka Kamata Dan Samun Wakilci Nagari.

Ya Kamata Matasa Su fi Kowa Yawa a Nade-Nade da Ake yi a Gamnatinsa, Saboda Gudummawar da Suke Bayarwa Kuma Sune Za su Kare Mutuncinsa, Kamar Yadda Yake Faruwa Kashi 70% Matasa Kuri`u Mafi Yawa Suka Kawo PMB Kan Mulki Amman Bamu da Kujerar Minista Koda Guda Daya, Wannan Abin Dubawa ne.

A Karshe Muna Addu’ar Allah Ya Kare PMB a Duk inda Yake.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *