Kafin Sohiyal Midiya Ta Jefa Nijeriya A Rijiya Gaba 1000

 

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Kowa ya san akwai babbar matsala a yanayin yadda muke amfani da kafafen sadarwa na zamani a wannan zamani. Zagi, Cin Zarafi da Sharri gami da Shifcin-gizo ya zama kamar wutar daji da ya ke neman kona Najeriya. Duk da matsalar ba a iya kafafen sadarwa na Hausa kadai suka tsaya ba, amma na HAUSA sun fi matukar muni sakamakon kaso mafi rinjaye na masu karantawa suna da karancin shekaru da ilimi da kuma wayewar zamani da ta addini. Ba sa iya rarrabe tsakanin labaran karya da na gaskiya, ko kuma mizanin hankali na gane kafafen sadarwa na gaskiya da na jeka-na-yi-ka.

Kamar yadda kaso mafi rinjaye na kafafen sadarwa da suke ikirarin su JARIDU ne na bogi ne, masu shafukan basu da alaka da aikin Jarida na nesa ko ta kusa. Ba su da mashawarta masu gogewa ko horon aikin Jarida. Ba su da ma’aikata masu horo akan harkokin kafafen yada labarai. Ba su da kowacce irin rajista da gwamnati ta jiha ko ta tarayya. Ba su da kishin kasa ballanatana ilimin sanin hakkokin al’umma da gwamnati.

Kawai kowa zai iya bude shafi a Facebook ya kira kansa da sunan JARIDA. Masaniya akan ka’idar rubutun HAUSA ma ba shi da ita. Aikinsa kawai ya kunna waya ya rika bi yana kwasar rubutun mutane yana malalawa a shafinsa. Ba ruwansa da wannan abin gaskiya ne, me ye madogarar mai rubutun, waye mai rubutun, me ya ke son isarwa a rubutun. Sannan kuma idan an wanki rubutun ba za a alakanta shi da mai rubutun ba. Copy and Paste shine babban Jigon mu. Idan an kwafo ba a da lokacin karantawa a ga akwai cin zarafin wani ko addinin wasu ko wata kabila. Ko wani abu da ya saba doka da zaman lafiya na al’umma. Kawai haka za a maka da sunan JARIDA.

Sannan a hana mutum Credit, kowa sai ya nuna shine ya mallaki Labari kamar WAHAYI ake yi masa. Sannan gwamnati kullum ihu take yi kafafen sadarwa na zamani akwai gagarumar matsala amma sun kasa daukar mataki. Muna ji muna gani yadda aka hura wutar rikicin jihar Filato da irin wadannan kafafen sadarwa na karya. Na tabbatar gwamnatin jihohi da na tarayya da masu ba wa shugaban kasa shawara akan harkokin Kafafen sadarwa na zamani sun ga rahoton BBC na yadda kafafen sadarwa suka ruwaito labaran karya a rikicin jihar Filato.

Wadannan hatsabiban kafafen sadarwa da dama an san masu ikirarin mallakar su, an san inda suke amma da yake ba a daukar al’amura da gaske an zuba musu ido. Ana kallo suna kirkirar karya mara tushe gami da koyawa matasa fitsara da rashin kunya. A zagi gwamna, a zagi Shugaban kasa, a zagi Sarakuna da Malaman addini da kowane mai mutunci. Ace kaza yayi kaza kuma karya ne ba a yi ba.

Yanzu dai ya rage ga gwamnati, kasashen duniya suna ta hankaltar da mu da kuma gwamnati. A dauki mataki ko kuma a jefa Nijeriya a cikin rijiya gaba 1000.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *