INEC Ta Gano Kulle-kullen Buga Katin Zabe Na Bogi

 

Daga Wakilinmu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta samu rahoton wani yunkurin buga katin zaben 2019 na bogi a rika saidawa ta kafafen sadarwa na online.

“Muna sanar da jama’a cewa, hukumar ta samu wannan rahoto kuma tana yin dukkanin kokari mai yiyuwa wajen daukar matakan kula da katinan zabe yadda ya kamata, da sauran kayayyakin hukumar daga bata gari.

“Da akwai hanyoyin tsaro da muka dauka da kuma lambobin sirri da ke tattare a jikin ainihin babban kati da hukumar ta samar, Wanda zai kare duk wani yunkurin kutse da za’a yi.

Amma shi wancan tallan katin zaben da ake yi ta na’urar zamani ya na bada damar ganin hoto ne kawai ba tare da sauran bayanai da hukumar zabe ta fitar ba.

“Wato ba ya dauke da hoton kowa kuma babu bayanin suna da sauran bayanan mai jefa kuri’a.”

Bisa ga wannan dalili hukumar na tabbatarwa jama’a da cewar ba ta dauki wannan batu da wasa ba, a bisa ga haka hukumar na sanar da gwamnati da sauran hukumomin tsaro da wadanda suke tallata wancan sanarwa cewa, cikin gaggawa a kawar da ita.

Sannan kuma za a bi salsalar masu tallata wannan harkalla ta shafukan su na tweeter domin gano masu wannan harkalla.

Bugu da kari akan haka, hukumar zabe ta sake daura damara wajen bada tsaro da kyakkyawar kulawa wajen kare katunan zabe na din din din daga kutse daga wasu, kuma muna tabbatar da cewa daga mako mai kamawa zamu kaddamar da sabbin hanyoyin kula da tantance dukkanin manyan katunan tantance masu jefa kuri’a da sauran kayayyakin ayyukan hukumar a fadin kasa gaba daya, kuma tuni wannan shiri ya samu nasara a jihohin Ekiti da Osun, a shirye shiryen gudanar da zabukan gwamnoni da za’ayi a jihohin biyu.

Muna kara sanar da ‘yan kasa cewar shirye shiryen hukumar sun yi nisa matuka wajen kula da kare dukkanin wani zabe da za’a gudanar yanzu har ya zuwa babban zabe na shekarar 2019 da ke tafe.

Sanarwa daga Oluwole Osaze Uzzi, Darakta na bangaren ilimin katin zabe da wayar da kan jama’a na hukumar.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *