Buhari, Dan Amarya Ba Ka Laifi

 

Daga Hajiya Jamila (Yar Baba Mataimaki)

Na rasa wace irin makauniyar soyayya ake yi wa wannan gwamnati na shugaba Muhammadu Buhari, inda sau da yawa akan tafka kura-kurai a mulkinsa amma makauniyar soyayya ta hana a fadi gaskiya.

Hujja daya tilo da zan iya kawowa a yanzu shine irin kashe-kashen rayukan da ake yi a yanzu, amma sai aka gagara fitowa fili a fadi gazawar gwamnatin Buhari a bangaren tsaro, sai ake danganta abin da ‘yan adawar siyasa.

Bana mancewa a lokacin gwamnatin Jonathan shi ma Buhari da kansa ya kalubalanci Jonathan da sakaci game da kashe-kashen da ake yi a karkashin gwamnatinsa ta PDP.

Don haka ya zama wajibi a fito a fadi gaskiya game da gazawar gwamnatin Buhari a bangaren tsaro, kamar yadda aka kalubalanci gwamnatin da ya gada game da matsala makamancin haka.

Idan har za a ce ‘yan adawa ne suke da hannu a wajen kashe-kashen da ake yi a yanzu domin batawa gwamnatin Buhari suna, kenan shi ma Jonathan ‘yan adawarsa ne suka dinga haddasa kashe-kashe domin batawa gwamnatinsa suna.

Adalci daya da ya kamata a yi shine, idan har an yarda da cewa masu adawa da gwamnarin Buhari ne ke haddasa wannan kisan, to shi ma Jonathan ba shi da laifi kenan a kisan da aka yi gwamnatinsa, wanda shine babban silar kayar da gwamnatin PDP.

Gaskiya dai daya ce, daga kin ta kuma sai bata.

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *