Ana zaben shugaban kasa a Mexico

Manyan 'yan takarar shugabancin kasar MexicoHakkin mallakar hotoREUTERS

Al’ummar Mexico na shirin kada kur’ia nan gaba a yau domin zaben sabon shugaba kasa da ‘yan majalisar wakilai 500 da kuma Sanatoci 128.

Hakazalika za a zabi gwamnoni da magadan gari.

Mutumin da ke kan gaba dai shi ne tsohon magajin garin birnin Mexico Andres Manuel Lopez Obrador.

Sai dai mummunan tashin hankalin da aka dade ba a ga irinsa ba ya mamaye yakin neman zaben.

Kawo yanzu an kashe ‘yan siyasa fiye da 130, tun lokacin da aka fara yakin neman zabe a watan Satumba.

Sai dai a yanzu da ranar yanke hukunci ta zo, wasu ‘yan kasar da dama na ganin wata dama ce a gare su ta kawar da gwamnatin da ta jefa su cikin wannan hali.

Da dama daga cikin ‘yan kasar ta Mexico, sun fusata da Enrique Peña Nieto da gwamnatinsa, kan jan kafar da tattalin arzikin kasar ke ciki, da karuwar cin hanci da rashawa, da aikata muggan laifuka da kuma take doka da oda.

Mutumin da ake ganin zai maye gurbinsa shi ne Andres Manuel Lopez Obrador, wanda ake wa lakabi da ‘AMLO’.

Shi ne ya zo na biyu a zabukan shugaban kasa biyu da suka gabata, kuma ya sanya batun yaki da cin hanci a sahun gaba a jerin abubuwan da zai aiwatar ta hanyar kara albashi da kudin fansho.

Ya ce za a samu kudaden yin hakan ne ta rage barna da almubazzarancin da ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa ke yi.

Abokin hamayyarsa Ricardo Anaya, ya yi kokarin bayyana Mr Lopez a matsayin mai ra’ayin ‘yan mazan jiya wanda ba zai iya rike amanar tattalin arzikin kasar ba.

Sai dai kuma kusan dukkan kuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa mafi yawan masu kada kuri’a ba su ji dadin wannan kiran ba, kuma a shirye suke su zabi Lopez Obrador, a karo na uku da ya ke bukatar kuri’arsu.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *