Ni ne zan iya kayar da Buhari – Kwankwaso

Rab'iu Musa KwankwasoHakkin mallakar hotoOTHER
Image captionSanata Kwankwaso na da magoya baya sosai musamman a arewacin Najeriya

Tsohon gwanman Kano kuma Sanata a jam’iyyar APC ya ce shi ne mutumin da ya fi kowa karfi da farin jinin da zai iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Injiniya Rab’iu Musa Kwankwaso ya shaida wa fitaccen dan jaridar kuma mawallafi, Dele Momodoushi yanzu ba shi da wata jam’iyya amma PDP ce ta fi kowacce dama da karfin kayar da shugaban, idan har ta ci gaba da bin tafarkin demokuradiyya.

“PDP na bukatar tsayar da mutumin da ya fito daga jihohin Kano, Katsina ko Kaduna takarar shugaban kasa idan har tana son yin nasara domin su ne jihohin da suka fi ko’ina yawan kuri’u,” in ji shi. Sannan ya ce shi ne ya fi kowa “cancantar yi wa jam’iyyar takara”.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar, wanda dan jihar Adamawa ne, da tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido, da na Kaduna Ahmed Makarfi, da na Kano Malam Ibrahim Shekarau na cikin wadanda suka bayyana aniyarsu ta neman takara a PDP.

Sai dai a kwanakin baya Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai kuma na hannun damar Shugaba Buhari, ya ce Kwankwaso ba zai iya hana Buhari lashe zabe a Kano ba a badi.

Kalaman na Kwankwaso na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ya kauracewa babban taron jam’iyyar APC na kasa, yana mai cewa an nuna ba a yi da shi.

Sanatan na cikin shugabannin bangaren tsaffin ‘yan PDP wanda ya kunshi Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, da na Wakilai Yakubu Dogara, da suka yi zargin ana muzguna musu a APC kuma gwamnatin Buhari ta mai da su saniyar-ware.

Zargin da jam’iyyar da gwamnatin suka musanta, kuma an fara tattaunawa domin duba korafe-korafen nasu.

  • Zuwa na taron APC zai iya haifar da abin kunya – Kwankwaso
  • Saraki ko Kwankwaso: Wa zai iya ja da Buhari a APC?
  • Gaskiya Kwankwaso ya taimake ni – Ganduje

Wannan ita ce alama mafi girma da kawo yanzu ta nuna inda jagoran na Kwankwasiyya, wanda ya dade yana rigima da tsohon mataimakinsa kuma mutumin da ya gaje shi a gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya nufa.

Domin ya nuna cewa zai iya komawa jam’iyyar PDP idan har za a bi tafarkin demokuradiyya wurin fitar da dan takarar shugaban kasa.

Sai dai masana na ganin kalaman na tsohon gwamnan da kuma take-takensa a baya-bayan nan sun nuna cewa tuni ya riga ya yanke wa kansa hukunci.

A makon da ya gabata ne aka rawaito cewa ya yi wata ganawar sirri da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a Abuja, sannan ya ziyarci jihar Ekiti don tattaunawa da Gwamna Ayo Fayose, inda kuma ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar PDP a zaben gwamman jihar da za a yi nan gaba a wannan watan.

Idan har Kwankwaso ya fice daga APC, to zai zamo dan siyasa mafi girma da ya bar jam’iyyar tun bayan ficewar Atiku Abubakar a watan Nuwamban bara.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *