Shin Adams Oshiomhole zai iya magance rikicin APC?

Oshiomhole shugaban APCHakkin mallakar hotoAPC
Image captionBa hamayya aka zabi Oshiomhole a matsayin shugaban APC

Tun kafin tabbatar da shi shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole ya ce shi ya fi dacewa ya magance rikicin APC.

To amma, ko tsohon gwamnan na jihar Edo zai iya hada kan ‘ya’yan jam’iyyar ta APC a yayin da wasu manyan ‘yan siyasa ke barazanar ficewa?

Wannan shi ne babban kalubalen da ake ganin ke gaban sabon shugaban jam’iyyar ta APC na kasa.

A ranar Asabar ne babban taron APC a Abuja, ba hamayya ya zabi Adams Oshiomhole a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

Oshiomhole ya samu goyon bayan Buhari da gwamnonin APC da kuma uban jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu wanda a baya aka ruwaito ya bukaci Odigie-Oyegun ya yi murabus.

Oshiomole wanda ya taba rike mukamin shugaban kungiyar kwadago a Najeriya, ya ce zai bi hanyar tattaunawa da fahimtar juna domin magance rikicin APC.

  • Ra’ayi Riga: Ta ya za a shawo kan rabuwar kai a jam’iyyar APC?
  • Zaben shugabannin APC ‘ya bar baya da kura’

Ana dai tafiya ne da sunan jam’iyya daya amma akwai masu hamayya da juna a APC musamman a jihohi da dama da jam’iyyar ke mulki.

An samu bangarorin APC da suka gudanar da nasu zaben shugabannin jam’iyyar na daban a matakin mazabu da kananan hukumomi da kuma jiha.

Sannan akwai takun-saka da ake tsakanin wadanda suka shigo jam’iyyar kafin zaben 2015 da ake kira ‘yan sabuwar PDP da kuma bangaren gwamnatin APC.

‘Yan sabuwar PDP dai sun yi zargin cewa ba a yi musu adalci a zabukan shugabannin da jam`iyyar ta yi a matakan kananan hukumomi da jihohi ba inda har suka yi barazanar ficewa daga jam`iyyar.

Hon. Yakubu Dogara da Sanata Bukola Saraki sun halarci babban taron jam'iyyar APC a AbujaHakkin mallakar hotoPRESIDENCY
Image captionHon. Yakubu Dogara da Sanata Bukola Saraki sun halarci babban taron jam’iyyar APC a Abuja

Duk da da cewa wasu daga cikin ‘yan sabuwar PDPn sun halarci taron na APC amma daya daga cikinsu tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kauracewa taron.

Kwankwaso wanda bangarensa ya gudanar da nashi zaben shugabannin jam’iyyar a matakin mazabu da kananan hukumomi da jiha, ya ce ya kauracewa taron ne saboda yadda jam’iyyar ta ki amincewa da zaben da suka gudanar.

Ya kara da cewa zuwansa na iya haifar da abin kunya da rikici a wajen taron.

Sauran rigingimun jam’iyyar sun hada da rikici tsakanin Kwankwaso da Ganduje a Kano da kuma rikicin Kaduna tsakanin bangaren gwamna El Rufa’i da Sanata Shehu Sani da sauran rikice-rikicen na APC a jihohin Kogi da Zamfara da Bauchi da Adamawa da Imo.

Taswira
Image captionJihohin da ke fama da rikicin siyasa a jam’iyyar APC

Amma a cikin jawabin da ya gabatar a wajen babban taron zaben sabbin shugabannin na APC, shugaba Buhari, duk da cewa bai ambaci sunan kowa ba a wajen taron, amma ya yi wani jirwaye mai kamar wanka, inda ya yi kira ga masu korafi da su kara hakuri.

“Rigingimun da muke fama da su, wadanda suka ki ci suka ki cinyewa, na faruwa ne sakamakon nasarar da jam`iyyarmu ke samu.”

“Ina kira ga dukkan masu korafe-korafe da su dinga yi wa jam`iyya kyakkyawan zato har zuwa lokacin da za mu daidaita al`amuranmu.” In ji shugaba Buhari.

Tun gabannin taron dai rahotanni ke nuna cewa jam`iyyar ta gwammace ta bi hanyar maslaha wajen zaben sabbin shugabannin, matakin da masharhanta ke ganin ba zai yi wa wani bangare na jam’iyyar dadi ba.

Jam`iyyar APC ta kuma kafa wani kwamiti na musamman, wanda kuma ya kebe lokaci, wato daga ranar 25 zuwa 27 ga wannan wata na Yuni domin sauraron korafe-korafe game da zabukan shugabannin da aka gudanar.

A shafinta na twitter, APC ta ce sabon shugabanta Adams Ashiomhole ya yi alkawarin magance rigingimun da jam’iyyar ke fama da su.

APC ta fada cikin rigingimun cikin gida tun bayan da ta lashe zaben shekarar 2015, lamarin da ya kai ga wasu ‘ya’yanta ficewa daga jam’iyyar baki daya, yayin da a yanzu wasu manyan jiga-jiganta ke barazanar ficewa.

A watan Fabrairu shugaba Muhammadu Buhari ya nada Bola Tinubu a matsayin jagoran dinke barakar da jam’iyyar APC ke fuskanta a fadin kasar. Amma har zuwa yanzu babu wani sasanci da aka kulla ko aka gani tsakanin bangarorin da ke rikici a jihohin na APC.

Rikicin na bangarori a jihohin APC da kuma barazanar ficewa daga bangaren ‘yan sabuwar PDP ya dada fito da girman kalubalen da ke gaban sabon shugaban jam’iyyar Adam Oshiomhole.

Masharhanta siyasa na ganin rigingimun jam’iyyar da ta ke fama da su na iya yi wa jam’iyyar illa sosai a zaben 2019.

Amma Mista Oshiomhole ya ce wani darasi ya samu a lokacin da yana jagorantar kungiyar kwadago shi ne bin matakai na shawarwari da kuma tattaunawa.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *