Faransa: An damke masu shirin kai hari kan Musulmi

French PoliceHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

‘Yan sandan Faransa sun damke wasu mutum 10 da ke da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu tsatsauran ra’ayi domin wani shirin da suka kitsa na kai hare-hare akan Musulmi.

An kama wasu daga cikin mutanen ne a wurare daban-daban cikin kasar, wasu kuma an kama su ne a tsibirin Corsica.

Hukumomin sharia’a a Faransa sun ce wadanda ake tuhuman shekarunsu na tsakanin 32 da 69 ne, sun kitsa wani gurgun shiri na kai munanan hare-hare akan Musulmai.

Hukumar leken asiri ta cikin gida ta Faransa – DGSI – ta bayyana yadda kungiyar ta ke kokarin sayan makamai, kuma ta gano gurnati da kayan hada bama-bamai a lokacin da jami’anta suka kai wani samame a gidan da wadanda ake tuhuman suke.

  • An samu raguwar masu shan taba sigari a Faransa
  • Jarumtakar da dan ci-rani ya nuna ta sa ya zama dan kasa a Faransa

Sun kuma bayyana cewa kungiyar ta shirya kai hari kan wasu wurare da suka hada da masu yin zazzafan wa’azi domin ya zama ramuwar gayya ga hare-haren da masu kishin Islama suka kai a Faransa.

Tun dai shekarar 2015 mutanen da aka ake sauya wa akida ke kai hare-haren da ke da nasaba da ayyukan jihadi a kasar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *