Najeriya: Yadda aka kashe mutum 86 a jihar Filato

Coffins are carried during a funeral service for 17 worshippers and two priests, who were allegedly killed by Fulani herdsmen in Benue State, north-central Nigeria on May 22, 2018.Hakkin mallakar hotoAFP/GETTY IMAGES
Image captionNajeriya ta dade ta na fama da rikici tsakanin makiyaya ‘yan kabilar Berom da kuma Makiyaya (tsohon hoto ne)

‘Yan sanda a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun ce akalla mutum 86 ne suka mutu bayan da fada ya barke tsakanin manoma da makiyaya.

Wasu rahotanni sun ce fadan ya barke ne ranar Alhamis bayan da ‘yan kabilar Berom suka farma wasu Fulani makiyaya, inda suka kashe biyar daga cikinsu.

Daga nan ne kuma aka ce wani hari na ramuwar gayya ya kai ga kisan wasu karin mutanen.

Yankin ya dade ya na fama da rikici tsakanin kabilun da ke rigima kan mallakar filaye.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin, sannan ya sha alwashin hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

Tun da farko an kashe gwamman mutane a wani rikici mai kama da wannan tsakanin Fulani da mafarauta a kasar Mali.

Tuni dai aka kafa dokar hana fita a wasu yankuna uku na jihar ta Filato.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Undie Adie ya ce binciken da aka gudanar a wasu kauyuka bayan kai harin ya tattabatar da cewa an kashe mutum 86, sannan wasu shida su ka samu rauni.

Ya ce an kona gidaje 50, da baburan hawa 15 da kuma motoci biyu.

Taswirar Jihar Filato

Kwamishinan yada labarai na jihar Yakubu Datti ya shaida wa BBC cewa dokar hana fitar za ta yi aiki daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe a Riyom, da Barikin Ladi da kuma Jos ta Kudu “domin hana jama’a daukar doka a hannunsu da samar da zaman lafiya”.

Sai dai sabanin bayanin ‘yan sanda, Mr Datti ya ce sama da mutum 20 ne suka jikkata, kuma suna samun magani a asibitoci daban daban.

Tare hanya

Rahotanni dai na cewa mutanen yankin da ake rikicin suna tare hanya su na kashe mutanen da ‘ba su ji ba, ba su gani ba,’ wadanda yawancinsu matafiya ne da ke fitowa daga jihohin arewa maso gabas kamar su Bauchi da Gombe da Yobe, zuwa Abuja.

Presentational grey line

Su wayeFulani Makiyaya?

A Fulani herdsman waters his cattle on a dusty plain between Malkohi and Yola town on 7 May, 2015Hakkin mallakar hotoAFP/GETTY IMAGES
Image captionWani makiyayi yana bai wa dabbobinsa ruwa
  • Suna daga cikin ƙungiyar makiyaya mafi girma a duniya kuma ana samun su a yammaci da kuma yankin tsakiyar Afrika, daga Senegal zuwa jamhuriyar Tsakiyar Afrika
  • A Najeriya wasu sun cigaba da zama a matsayinsu na makiyaya, yayin da wasu suka koma birane
  • Fulani makiyaya suna yin akasarin rayuwarsu a daji ne, ba kamar mutanen da ke zama a cikin birane ba, kuma suna da alaƙa da waɗannan rikice-rikicen
  • Suna kiwon dabbobinsu a yankuna da dama, inda suke yawan yin rikici da al’ummomin da galibin aikinsu noma ne
  • Ana yawan dangantasu da ƙabilar Hausa, saboda tsawon lokacin da suka shafe suna zama tare
  • Fulani sun taka muhimmiyar rawa a ƙarni na 19 wajen farfaɗo da addinin Musulunci a Najeriya.

Me ke kawo rikicin?

Ana tunanin ce-ce-ku-ce a kan abubuwan more rayuwa kamar su gonaki da yankunan da ke da burtali da ruwa ne ke jawo rikici tsakanin makiyaya da kuma manoma.

Fulani makiyaya kan iya tafiya mai nisa tare da dabbobinsu domin nema musu abinci. Mafi yawan lokuta, suna daukar makamai domin kare dabbobin nasu.

Wasu matafiyaHakkin mallakar hotoOTHER
Image captionRikicin ya rutsa da matafiya da dama kamar wadannan da ba a tantance ko su wa ye ba

Suna yawan rikici da manoma wadanda ke yawan cewa suna lalata musu amfanin gona kuma ba sa kula da inda dabbobin nasu ke zuwa.

Fulanin na zargin cewa manoma waɗanda ke ƙoƙarin satar shanunsu – suna cewa suna ƙoƙarin kare kansu ne.

A da, rikicin a yankin tsakiyar Najeriya aka fi yi, inda kiristoci ƙabilar Birom da ke jihar Plateau suke kisan ramuwar gayya ga Musulmai da makiyaya.

Yadda sauyin yanayi ya ke shafar burtali ya sa Fulani makiyaya sun kara matsawa zuwa kudancin Najeriya domin neman ruwa da ciyawa.

Wannan ya ƙara faɗaɗa rikicin ta inda ake cigaba da fuskantar munanan tashe-tashen hankula a kudancin ƙasar, ana ƙara jin tsoron cewar rikicin zai yi barazana ga haɗin kan da dama ya ke tangal-tangal tsakanin ƙabilun Najeriya.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *