Shugaban Zimbabwe Mnangagwa ya tsallake rijiya da baya

Reports
Shugaban Zimbabwe Emmerson MnangagwaHakkin mallakar hotoEPA
Image captionAn kai harin ne a yayin da Mnangagwa ke yakin neman zabensa.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya tsira daga wani harin bom da aka kai a yayin da yake gangamin yakin neman zabensa a garin Bulawayo.

Mista Mnangagwa ya ce wani abu “ya fashe kusa da ni – amma lokaci na bai yi ba.”

Hoton Bidiyo daga filin wasa na White City ya nuna faruwar fashewar a kusa da Mista Mnangagwa a yayin da yake barin mumbarin da ya yi wa magoya bayansa jawabi.

Ko da yake ba abin da ya samu shugaban, amma kafar talabijin din kasar ta ruwaito cewa mataimakinsa Kembo Mohadi ya samu rauni a kafarsa.

Shugaba Mnangagwa wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin a shafinsa na twitter ya ce ya ziyarci wadanda suka samu rauni a asibiti. Sannan ya yi Allah wadai da harin tare da yin kira ga hadin kan kasa.

Mnangagwa ya zama shugaban Zimbabwe a watan Nuwamban da ya gabata bayan hambarar da tsohom mai gidansa Robert Mugabe.

Shugaban ya tafi Bulawayo gari na biyu mafi girma a Zimbabwe kuma yankin da ‘yan adawa suka fi karfi domin yakin neman zabensa.

A ranar 30 ga Yuli ake sa ran gudanar da babban zabe a Zimbabwe.

Zaben zai kasance na farko tun bayan hambarar da gwamnatin Mugabe wanda ya shafe shekaru 37 yana shugabanci a kasar.

Red CrossHakkin mallakar hotoEPA
Image captionJami’an Red Cross suka kwashe wadanda suka ji rauni

Kafofin yada labaran Zimbabwe sun ruwaito cewa harin ya rutsa da shugaban jam’iyyar Zanu PF Oppah Muchinguri-Kashiri, da kuma wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Taswirar Zimbabwe

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *