2019: An Kama Bakin-haure Sama Da 300 Wurin Kokarin Yin Rajista -INEC

 

Daga Wakilinmu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa sama da jam’iyyun siyasa 100 ne ake sa ran za su fito takarar mukamai daban-daban a zaben 2019.

Shugaban Hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a wani taron wayar da kai da wasu kungiyoyi suka shirya ga masu ruwa da tsakin zabe jiya Alhamis a Abuja.

Kungiyar Kula da Batutuwan Zabe ta TMG, sai kuma DFID da V2P ne suka shirya taron.

Yakubu y ace ya zuwa yanzu jam’iyyu 138 ne suka nemi a yi musu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.

Baya ga wannan kuma, ya bayyana cewa jami’an kula da shige-da-fice sun damke bakin-haushe ‘yan wata kasa sama da 300 da aka kama sun a kokarin yin rajistar damar kada kuri’a a Najeriya.

“Ya zuwa ranar 24 Ga Mayu, an samu karin yi wa mutane milyan 9 rajista a kasar nan. Wannan ya karo adadin wadanda ke da rajista a Najeriya sun kai kimanin milyan 80 kenan.

“INEC ta na hada kai da karfi da jami’an tsaro domin dakilewa da bincike da damke masu sayen kuri’u da kudin a lokacin da ake zabe.” Inji Yakubu.

A karshe ya ce INEC ba ta da karfin ikon da za ta hana kowace kungiya fitowa ta yi rajistar zama jam’iyya, matukar dai ta cika sharuddan da doka ta gindaya na yin rajistar jam’iyya.

Idan ba a manta ba, a farkon wannan shekara, INEC ta tabbatar da cewa yawan jam’iyyun siyasa ba zai kawo wa hukumar wani cikas yayin gudanar da zaben 2019 ba.

…. INEC za ta gurfanar da duk wanda ya sayi kuri’u a zaben Gwamnan Osun

A wata sabuwa kuma, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi kakkausan gargadin cewa za ta yi amfani da jami’an tsaro domin ta cafke kuma ta maka duk wanda ta kama ya na sayen kuri’u a zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar nan gaba.

Kwamishinan INEC na Jihar Osun, Olusegun Agbaje ne ya bayyana haka a cikin wannan makon a lokacin da yake taron ganawa da shugabannin jm’iyyun siyasa dangane da shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Osun da za a yi a ranar 22 Ga Satumba, 2018.

Agbaje ya ce INEC ta shirye tsaf domin ta gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe, wanda zai karbu hannu biyu daga kowane bangare. Ya ci gaba da cewa za a yi amfani da na’urar nan ‘yar-kure domin tantance masu kada kuri’a, wato Card Reader.

Ya ce rashin nuna da’a da dattakon da ‘yan siyasa ko jam’iyyun siyasa ba su yi wa dimokradiyya, abu ne mai matukar illa ga tsarin zabe.

Don haka sai ya yi kira da jam’iyyu su rika nuna kawaici da dattako domin ci gaban tsarin dimokradiyya.

Ya ce abin damuwa ne ganin yadda wasu ‘yan siyasa ba su da wani jarin kara wa dimokradiyya nagarta, sai ma kokarin kawai su sai sun ci zabe ko da tsiya.

Agbaje ya ce haifar da tashin hankali da dabanci a lokacin zabe abubuwa ne masu lalata nagartar tsarin dimokradiyya.

Ya ce da masu satar akwatu da masu sayen kuri’u su ma wani bangare ne da ke illata tsarin zabe.

Daga nan sai ya ce duk wanda ya sake aka kama shi ya na sayen kuri’un jama’a, to ya kuka da kan sa.

Ya ce jami’an tsaro za su damke shi kuma a maka shi kotu domin ya zama darasi ga wasu.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *