TAKAITACCEN JAWABIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI A LOKACIN DA YAKE SANYA HANNU A KASAFIN KUDI NA 2018 YA ZAMA A FADAR GWAMNATIN TARAYYA DA KE ABUJA

News

Takaitawa daga Nishadi TV

Da farko shugaba Buhari ya gode ma ‘yan majalisun kasa musamman shugabaninsu wato shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da na majalisar wakilai, Yakubu Dogara bisa jajircewarsu wajen ganin kasafin kudin ya zama doka.

Shugaban ya ce a lokacin da ya aike wa da majalisun daftarin kasafin kudin na 2017 a ranar 7 ga watan Nuwamba 2017 ya dauka cewa majalisun za su yi sauri dubawa da amincewa don a aiwatar da shi da wuri amma hakan bai samu ba.

Buhari ya nuna bacin ransa da canja-canjan da majalisar dokokin tarayya ta yi ckin kasafin kudin na rage-rage da kare-kare.

Ya kuma ce, “Abin takaici, babu mutunci cikin abin da suka dawo min da shi. Majalisun tarayya sun zabge kudi Naira bilyan 347 cikin ayyukan 4,700 da aka gabatar ma ta amma suka sanya ayyukan kansu guda 6,403 na kimann kudi Naira bilyan 578.”

A cewarsa “Da yawa daga cikin ayyukan na da muhimmanci kuma zas u yi wuyan zantarwa da irin wannan zabgewa da majalisa ta yi.

“Wasu daga cikin sabbin ayyukan da ‘yan majalisa suka sanya ba a duba su da kyau ba, ba a tsara su da kyau ba, kuma za su yi wuyan aiwatarwa.”

Haka kuma shugaban ya cigaba da cewa, da yawa daga cikin ayyukan da ‘yan majalisun tarayya suka kara cikin kasafin kudn ma’aikatu, an kara ne ba tare da la’akari da karfin ma’aikatun ko za su iya ba ko kuma za su bukaci karin ma’aikata domin aiwatar da su.”

Bugu da kari Buhari ya ce “A yanzu haka, wasu daga cikin ayyukan da ‘yan majalisa suka kara cikin kasafin kudin hakkin jihohi ne da kananan hukumomi wanda babu ruwa gwamnatin tarayya da su.

Kasafin kudin dai da yawansa ya kai Naira tirilyan 9.12 wanda ya fi na shekara 2017 da kashi 22.6 cikin dari kuma wanda ba a taba kasafin kudi da ya kai yawan haka ba a tarihin Najeriya.

Shugaban ya godewa Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa da kuma ofishin kasafin kudi na tarayya da duk wani wanda ya bayar da gudunmuwa wajen tabbatar da yiwuwar wannan aiki na kasafin kudi wanda da ba dominsu ba da aikin ba zai yiwu ba.

Ya kuma yi alkawarin wajen inganta ‘yan kasa da kuma kyautatawa ba wai kawai ga shirya kasafin kudi ba wajen tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin kudin.

Daga karshe ya godewa kowa da kowa, ya kuma roki Allah ya sanyawa Najeriya albarka.

Fassara da takaita jawabin daga www.nishadi.tv
Shafin Farko
nishadi.tv

@Rariya

Leave a Reply

Your email address will not be published.