Jarumi dan ci-rani zai gana da shugaban kasarsa ta asali

Mamoudou Gassama lokacin da a hau ginin domin ya kubatar da yaron .Hakkin mallakar hotoFACEBOOK
Image captionDan ci-rani daga Mali

Dan ci-rani dan asalin kasar Mali, wanda ya nuna jarumta wajen ceto wani jaririn da ya makale a saman wani bene a birnin Faris, zai gana da shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta, a ranar Litinin.

Mamadou Gassama, wanda aka yi wa lakani da “mai yanar gizo” domin jarumtakar da ya nuna, ya koma Mali inda aka masa tabar gwarzo kamar yadda wannan sakon Twitter din ya nuna:

Ana sa ran zai koma Faransa domin rattaba hannu kan takardar aiki da hukumar ‘yan kwana-kwana ranar 28 ga watan Yuni.

  • Jarumtakar da dan ci-rani ya nuna ta sa ya zama dan kasa a Faransa

Mista Gassama, wanda ya kasance bakon haure, ya samu izinin zama dan kasar Faransa tare da aikin dan kwana-kwana bayan ya samu yabo domin hawa bene hudun da ya yi a watan jiya domin ceto wani yaro dan shekara hudu.

Mista Gassama ya ja hankalin duniya ne bayan an yi ta yayata bidiyon ceton ban mamakin da ya yi.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *