‘Hare-haren kunar bakin-wake sun kashe mutum 31 a Borno’

Taswirar Damboa

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hare-haren kunar bakin wake a jihar Borno.

An kai hare-haren ne a garin Damboa a ranar Asabar washegarin Sallah da dare.

Zuwa yanzu babu cikakken bayani game da yawan mutanen da suka mutu amma hukumar agajin gaggawa NEMA ta ce akalla mutum 20 suka mutu.

Wasu rahotanni kuma sun ce kimanin mutane 31 suka mutu, yayin da gwammai suka jikkata.

Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa ‘yan kunar bakin wake shida ne, dukkaninsu ‘yan mata, suka kai hare-haren ranar Asabar da dare inda suka kashe mutane akalla 20 da jikkata wasu fiye da 40.

Rahotannin sun ce bayan harin kunar bakin wake, mayakan kuma sun bude wuta ga taron jama’a a Damboa da ke bikin Sallah tare da harba gurneti.

Biyu daga cikin ‘yan kunar bakin waken sun kai harin ne a Shuwari kusa da Abashari, inda suka kashe mutum shida, kamar yadda Kamfanin dillacin labaran AFP ya ambato Babakura Kolo shugaban ‘yan kato da gora a Borno yana cewa.

“Yanzu mutane 31 suka mutu, kuma adadin na iya karuwa saboda wadanda suka ji mummunan rauni suna yanayi na rai-kwakwai-mutu-kwakwai.” in ji shi.

Ya ce mutane da dama sun samu rauni ne daga gurnetin da aka harba a taron jama’a a wajen garin Damboa.

  • Ban da karfin ba jami’an tsaro umurni – Gwamnan Zamfara
  • ‘Sayyadina Umar ya taba aika sako Daular Borno’

Hukumar NEMA ta ce an tura jirage masu saukar Angula na Majalisar Dinkin Duniya domin kwaso wadanda al’amarin ya shafa zuwa Maiduguri.

Harin ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan kuma na zuwa a yayin babban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai ya yi kira ga ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da su koma gidajensu saboda an tabbatar da tsaro a yankin.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *