Kun san me Buhari ya tattauna da gwamnonin APC?

Buhari da Gwamnonin APCHakkin mallakar hotoPRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jam’iyarsa ta APC a fadarsa da ke Abuja.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha bayan ganawar, ya shaida wa manema labarai cewar sun tattauna batutuwan da suka shafi APC, musamman batun babban taron jam’iyyar da ke tafe.

Sai dai bai yi cikakken bayani game da abin da ganawar ta kunsa ba.

Amma gwamnan na Imo ya kuma ce sun zo ne domin yaba wa Shugaba Buhari kan matakinsa na amincewa da ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimukradiya da kuma karrama Moshood Abiola.

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar a Abuja, a ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da aka soke.

  • APC ‘ta rabu biyu’ a wasu jihohi
  • APC ta sha kaye a hannun PDP a zaben jihar Oyo
  • Shugaba Buhari ya nemi afuwa kan Abiola

Gwamnonin da suka halarci ganawar sun hada da na Zamfara da Kaduna da Kebbi da Kano da Jigawa da Kogi da Katsina.

Sauran sun hada da gwamnonin Imo da Kwara da Adamawa da Ogun da kuma Benue.

An yi ganawar ne a ranar Talata da dare a dakin taro na uwar gidan shugaban a Villa.

Ana ganin dai ganawar ba ta rasa nasaba da tattauna yadda za a magance rikicin cikin gida da jam’iyyar APC ke fama da shi a wasu jihohi a yayin da zaben 2019 ke karatowa.

Rikicin cikin gida a wasu jihohi da dama na APC ya yi tasiri a zabukan shugabannin jam’iyyar a mataki na kananan hukumomi da mazabu da aka gudanar a kwanakin baya.

Wasu bangarori na APC a jihohin da dama da suka hada da Kano da Adamawa da Bauchi da Zamfara sun gudanar da nasu zaben ne na daban na shugabanin jam’iyyar a kananan hukumomi.

Masharhanta siyasa na ganin rigingimun da jam’iyyar da ta ke fama da su a jihohi na iya yi wa jam’iyyar illa sosai a zaben 2019.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *