FBI ta kama wasu ‘yan Najeriya da laifin zamba a intanet

FBIHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Hukumar tsaro ta Amurka, FBI ta ce ta kama wasu mutane fiye da 70 ciki har da ‘yan Najeriya, wadanda ake zargi da zambar miliyoyin daloli ta hanyar intanet.

Hakan ya biyo bayan wani hadin guiwa da FBI din ta yi da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFFC a Najeriya.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet, inda tace ta samu karbo kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka kusan miliyan 2.5.

Sannan ta samu katse wasu sakonni na kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 14 da ake shirin turawa.

Ana zargin mutanen da aika wasiku ta hanyar intanet inda suke angulu da kan zabo suka kuma damfari wasu Amurkawa.

Aikata manyan laifuka ta hanyar intanet dai babbar matsala ce a Najeriya, lamarin da ya jima yana bata sunan kasar a kasashen ketare.

  • A wacce kasa fetur ya fi araha da kuma tsada a duniya?
  • An daure tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye shekara 14

Cikin mutanen 74 da hukumar ta FBI ta kama sun hada da ‘yan Najeriya 29 da wasu ‘yan kasashen China da Mauritius da kuma Poland.

Mr. Wilson Owujaren shi ne kakakin hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati ta EFCC ta Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa: “Mun yi aikin hadin guiwa tare da FBI a Lagos tsakanin ranar 23 ga watan Mayun da ya gabata zuwa ranar 7 da watan Yunin da muke ciki.

“Ba zan ce ga adadin mutanen da abin ya shafa ba. Amma zan iya tabbatar muku da cewa mun damke wasu mutane kuma muna ci gaba da bincikensu.”

Wannan layi ne

Yaya suke wannan lamari?

dollarHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Mista Uwajaren ya kara da cewa: “Damuwarmu ta shafi abin da ake kira wasikun email na kasuwanci. Wata hanyar zamba ce inda masu yin ta ke fakon mutanen da ke tura sakonnin kudi ta hanayar intanet.

“Sai su datse bayanan da ake yi tsakanin mai aika sakon da wanda za a aikawa. Kuma da zarar sun samu bayanka sai su sauya bayanan asusun ajiyar kudadenka daga nan kuma sai su kwashe kudaden.

“Yawanci sun fi zambatar ‘yan kasashen waje, shi yasa ma hukumar FBI ta shiga cikin binciken. Kuma kungiya ce babba wadda ke ayyukanta ba kawai a Najeriya ba har ma da wasu kasashen duniya.”

Hukmar FBI ta ce ta kwashe tsawon wata shida tana bin diddigin ayyukan masu zambar kafin ta kai ga kama mutanen wadanda wasunsu ‘yan Najeriya ne mazauna Amurka.

Tuni dai har an gurfanar da wasu mazauna jihohin Dallas da Texas, inda ake tuhumar wasu daga cikinsu da zambatar wani lauyan kamfanin dillancin gidaje na fiye dala dubu 240, kuma suka halatta kudaden haram da yawansu ya kai sama da 600,000.

Matsalar aikata miyagun laifuka ta hanyar intanet, matsala ce da ke ci gaba da ci wa hukumomi tuwo a kwarya, a yayin da ake samun ci gaba ta fuskar fasaha a duniya.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *