Kwastam ta kama manyan motoci makare da shinkafa

News
Akasari daga shinkafar tana shigowa daga jamhuriyar Benin ne.
Image captionBincike ya nuna ana hada baki da direbobin kamfanonin sarrafa barasa domin fasa kwaurin shinkafa ‘yar waje.

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Kwastam, da ke kula da shiyyar kudu ma so yammacin kasar ta ce a baya-bayan nan ana kara kama manyan motoci mallakar manyan kamfanonin cikin gida makare da shinkafa ‘yar waje.

Wannan dai ya zo ne bayan da hukumar kwastam din ta kama manyan motocin kamfanonin Dangote da kuma kamfanin da ke sarrafa barasa na Nigerian Breweries makare da shinkafa ‘yar waje da aka shigo da ita daga bakin iyakar kasar ta Jamhuriyar Benin.

Kontirola na kwastom mai kula da shiyyar kudu ma so yammacin kasar ya ce: “Mu na kyautata zato wadannan kamfanoni ba su kafa kamfanoninsu domin yin fasa kwaurin shinkafa ba. Mun kama shinkafa wacce direbobi suka boye.

  • Shekara uku na mulkin Buhari ‘ba yabo ba fallasa’
  • Najeriya ta ceto yara 10 daga masu safarar mutane zuwa Rasha
  • Najeriya da Ghana ne inda aka fi zub da ciki a duniya

“Mu na kyautata zato kamfanonin ba su da hannu, sai dai mun gano yadda bara-gurbin dirobobi ke amfani da motocin kamfanonin Dangote da kamfanin sarrafa barasa domin fasa kwaurin shinkafar.”

Ana anfani da manyan motocin domin shigo da shinkafa mai yawa
Image captionAn kama manyan motocin `kamfanonin Naijeriya biyu da fasa kwaurin shinkafa ‘yar waje.

A yanzu haka dai hukumar kwastam da ke a kudu maso yammacin kasar a karkarkashin Kontirola Muhammad Uba Garba na tsare da wasu direbobi, kuma nan gaba za a gurfanar da su a gaban shari’a.

Me kamfanonin ke yi akan wadannan direbobi?

Kamfanonin dai sun sha tsame hannunsu daga abin kunya kamar wannan.

Sa’annan sun sha jan kunnen direbobin cewa kar su kuskura su yi amfani da dukiyar ko motocin kamfanoninsu domin aikata wasu abubuwa da su ka yi hannun riga da fadar dokar kasa.

Kamfanonin sun kuma sha hukunta direbobi da ake kamawa da hada baki da ‘yan fasa kwauri domin shigo da shinkafa Najeriya.

Yanzu haka dai hukumar kwastam ta kama direbobi biyu kuma suna ci gaba da yin karin haske tun bayan haduwa da fushin hukuma.

Gwamnatin tarayya ta haramta shigo da shinkafa ‘yar kasashen waje a wani yunkuri na bunkasa noman shinkafa a cikin gida.

To amma duk da haka ana samun wasu da ke cin gajiyar shigo da shinkafar ta hanyar yin fasa kwaurinta cikin kasuwannin Najeriya.

A wannan shekara kadai an kama shinkafa ta biliyoyin nairori duk kuwa da a cikin gida ana noma ta har ma ana ketarawa da ita domin sayar wa ga kasashen duniya.

A baya dai kafin shigowar gwamnatin Muhammadu Buhari, Najeriya ta dogara da ciyar da al’ummar ta abinci daga shinkafar da aka shigo da ita. Sai dai a yanzu gwamnati ta haramta shigo da shinkafa ta kan tudu, sai dai ta gabar teku.

Amma rahotanni sun nuna akwai yiwuwar kafin karshen shekarar 2019 gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da shinkafar ‘yar waje daga sassan da ke a gabar teku da kuma ta tudu.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *