Julen Lopetegui ne sabon kocin Real Madrid

Kocin Madrid Julen LopeteguiHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionLopetegui ya zama kocin tawagar kasar Spain a shekarar 2016

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nada Julen Lopetegui a matsayin sabon kocinta.

Kungiyar ta fara neman sabon koci ne tun bayan da Zinedine Zidane ya bar kulob din a watan da ya gabata.

Sabon kocin, mai shekara 51, ya kulla yarjejeniyar shekara uku ne a kungiyar wadda za ta fara aiki bayan kammala Gasar Cin Kofin Duniya.

Lopetegui ne zai jagoranci Spain a gasar.

Lopetegui wanda tsohon kocin kungiyar Porto ne ya taba kasancewa da karamar kungiyar Real Madrid kuma sau daya ya taba yi wa babbar kungiyar wasa.

A karshen watan Mayu ne Zinedine Zidane ya ajiye aikin horar da Real Madrid, kwana biyar bayan ya lashe Kofin Zakarun Turai a karo na uku a jere.

  • Da gaske ne Mo Salah zai koma Real Madrid?
  • Daliban Shari’a sun yi jarabawa a kan Ramos da Salah
  • Yadda murabus din Zinedine Zidane ya girgiza Real Madrid. BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *