An daure tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye shekara 14

Joshua DariyeHakkin mallakar hotoEFCC
Image captionJoshua Dariye ya mulki jihar Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017

Wata kotu a Najeriya ta daure Tsohon Gwamnan Filato Joshua Dariye shekara 14 a gidan yari bayan ta same shi da laifin cin amana da almubazzaranci.

Mai shari’a Adebukola Banjoko ta samu Mr Dariye, wanda sanata ne da ke wakiltar Filato ta tsakiya, da laifi a kan tuhumce-tuhumce 17 daga cikin 23 da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta zarge shi da aikatawa.

Laifukan sun hada da almubazzaranci da halatta kudin haram a lokacin da ya mulki jihar ta Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017.

Sanata Dariye ya kasance cikin damuwa da dimuwa a lokacin da ake karanta hukuncin, ya nemi lauyan EFCC ya nuna tausayi da afuwa a matsayinsa na mai bin addinin Kirista.

Wannan hukunci na zuwa kwanaki kadan bayan da mai Shari’a Banjoko ta daure tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame shekara 14 a gidan yari saboda almubazzaranci da zamba da halatta kudin haram.

An yanke masa shekara 14 saboda cin amanar duniyar jama’a, sannan shekara biyu saboda almubazzaranci da dukiyar gwamnati.

Za a hade hukuncin wuri guda, wanda hakan ke nufin zai yi zaman jarum na shekara 14. Kuma ba a bashi zabin biyan tara ba.

 • Kotu ta samu Joshua Dariye da laifin almundahana
 • An yanke wa tsohon Gwamna Jolly Nyame daurin shekara 14
 • Shin tsoffin gwamnoni nawa EFCC ta kai kotu?

Mr Dariye ya yi shiru yana saurare a lokacin da ake karanta hukuncin a babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke unguwar Gudu.

Mai shari’a Bamijoko ta ce Sanata Dariye ya barnatar da sama da naira biliyan daya da aka bai wa jihar domin shawo kan matsalar zaizayar kasa.

Mai shari’ar ta ce tsohon gwamnan ya fi jiharsa kudi, a don haka “babu wata hujja ta aikata cin hanci da rashawa ta kowacce fuska ga mai kudi ko talaka”.

‘Izina ga ‘yan baya’

Lauyansa Kanu Agabi ya soki sahihancin shaidun da aka yi amfani da su wurin samunsa da laifi, amma mai shari’ar ta ce shaidun sun tabbatar da almundahanar da aka tuhume shi da aikatawa.

line

Bayanan lauyoyi

Lauyan hukumar EFCC Rotimi Jacobs ya nemi mai shari’ar da ta yanke wa tsohon gwamnan mafi tsaurin hukunci saboda barnar da ya aikata.

Ya ce Mr Dariye ya dade yana yawo da hankalin masu shari’a kan batun, abin da ya sa kotun kolin kasar ta yi Allah-wadai da halayyarsa a baya.

Ya kara da cewa ganin yadda aka dade ana yin wannan shari’a tun shekarar 2007, ya kamata a yankewa sanatan hukunci mai tsauri domin ya zama izina ga ‘yan baya.

Sai dai a nasa bangaren, lauyan wanda ake tuhuma Kanu Agabi, ya nemi kotun da ta yi wa mutumin da yake karewa sassauci, yana mai cewa an wanke shi daga cikin kashi 40 cikin dari na laifukan da aka tuhume shi.

Abin da ya ce ya nuna cewa Sanata Dariye ba mutumin banza ba ne.

Ya kara da cewa tsohon gwamnan ya samu kansa a wannan hali ne saboda rashin fahimtar kundin tsarin mulkin Najeriya domin ya hau mulki ne a lokacin da dimokuradiya na jaririya.

A don haka ya nemi mai shari’ar da ka da ta yanke masa hukunci mai tsauri irin wanda ta yi wa Jolly Nyame.

Sai dai lauyan EFCC ya yi watsi da wannan bukatar.

line

Wane ne Joshua Dariye?

Joshua DariyeHakkin mallakar hotoEFCC
 • Bayanai sun nuna cewa an haife shi ne a watan Yulin 1957
 • Ya fito daga Karamar Hukumar Bokkas ta jihar Filato
 • Ya yi fice a harkar kasuwanci kafin ya shiga siyasa
 • Rahotanni sun ce ya kashe kudi wurin tallafawa takarar Olusegun Obasanjo a 1999 da 2003
 • An zabe shi gwamna a jam’iyyar PDP a shekarar 1999
 • Ya sake cin zabe karo na biyu a 2003
 • A Nuwamban 2006 ne ‘yan majalisar jihar suka tsige shi
 • Kotun koli ta mayar da shi kan kujerarsa a watan Afrilun 2007
 • An zabe shi sanata a jam’iyyar Labour a 2011 domin wakiltar Filato ta tsakiya
 • An shafe shekara 11 ana shari’ar wacce aka fara a 2007. BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *