Spain za ta ‘karbi ‘yan ci-ranin’ da Italiya ta ki karba

Migrants picked up by the AquariusHakkin mallakar hotoSOS MEDITERRANEE
Image captionKungiyar agaji ta SOS Méditerranée ta wallafa hotunan ‘yan ci-ranin da aka ceto

Firai ministan Spaniya ya ce kasarsa za ta karbi jirgin ruwan da ya ceto ‘yan ci-ranin da suka makale a tekun Mediterranean, domin ganin ba su fada cikin mummunan bala’i ba.

Pedro Sánchez ya ce zai bayar da “matsuguni” ga Aquarius da kuma mutum 629 da ke cikinsa, bayan da Italiya da Malta suka ki su bai wa jirgin izinin shiga kasarsu.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da kuma Tarayyar Turai sun yi kiran da aka kawo karshen takaddamar da kasashe biyun ke yi cikin gaggawa.

Mr Sánchez, wanda ya hau mulki a makon da ya gabata, ya ce jirgin zai sauka a birnin Valencia.

  • Najeriya ta ceto yara 10 daga masu safarar mutane zuwa Rasha
  • Bakin-haure sama da 6,000 sun makale a teku

An debo ‘yan ci-ranin ne daga wasu kananan jiragen ruwa a gabar ruwan Libya a karshen mako, a wani aikin ceto guda shida, kamar yadda kungiyar agaji ta Jamus SOS Méditerranée ta bayyana.

“Hakkinmu ne mu ga an kaucewa aukuwar bala’i sannan mu samar da wuri ga wadannan mutane, kamar yadda dokokin kare hakkin bil’adama suka nemi mu yi,” a cewar Mr Sanchez.

Ko a ranar Asabar baki sama da 100 aka ceto daga teku bayan jirgin da ke dauke da su ya samu matsala.

Su wa ye a cikin jirgin?

Wadanda suak tsira sun hada da matasan da ke tafiya su kadai 123, kananan yara 11 da kuma mata masu juna biyu su bakwai, a cewar SOS Méditerranée.

Shekarun matasan sun kama daga 13 zuwa 17 kuma sun fito ne daga Eritrea, Ghana, Najeriya da Sudan, kamar yadda wani dan jarida da ke cikin jirgin, Anelise Borges, ya ce.

Ya shaida wa BBC cewa “Kusan dukkansu sun gaji matuka, sun samu kansu a wani mawuyacin hali saboda sun shafe sa’a 20 zuwa 30 a teku kafin a tserar da su”.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *