Zamfara: Mutane na yin kaura saboda ‘yan bindiga

Jihar Zamfara a tarayyar Najeriya

Daruruwan mutane na yin kaura zuwa makwabtan jihohi kamar Katsina sakamakon karuwar ayyukan ‘yan bindiga.

Banda ‘yan bindiga akwai kuma matsalar masu satar mutane don neman kudin fansa.

Al’amarin, a cewar wasu mazauna garuruwan jihar ya kai har da rana tsaka ‘yan bindiga na iya zuwa su sungumi mutum zuwa daji har sai an biya kudin fansa.

Wani mazaunin karamar hukumar Shinkafi, Sulaiman Shu’aibu Shinkafi ya shaida wa BBC cewa matsalar ta na neman fin karfinsu.

“Tura ta kai bango, matsala ta taso mana, wanda tun ana yi kauyuka har an kai yau sai a shiga Shinkafi da bindigogi, da manyan makamai a dauki mutum a tafi da shi.”

Kwanan baya aka lalata bindigogi karkashin wani shirin yin afuwa da gwamnati jihar ta bullo da shi a bara
  • ‘Gwamna yana limanci amma ana kashe bayin Allah a Zamfara’
  • An sake kashe mutum 23 a Zamfara
  • An sace iyalan wani kwamishina a Zamfara

Sulaiman Shu’aibu Shinkafi ya kuma koka da cewa, “Mutane na kallo ba abin da za su iya yi saboda da manyan makamai suke zuwa.”

Rahotanni sun ce da misalin karfe daya da rabi na dare mahara suka shiga garin na Shinkafi suna harbe-harbe.

“Sun dauki wani dan uwanmu da karfin tsiya tare da sakataren karamar hukumar Shinkafi, kuma sun tafi da su daji. Sun kuma sake daukar wani kaninmu.”

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *