‘Yadda na rayu bayan uwata ta zub da cikina tana zaton na mutu’

Melissa Ohden
Image captionMelissa Ohden ta gane cewa an zbuda cikinta

A lokacin da Melissa Ohden take ‘yar shekara 14 ta ji wani boyayyen labari mai tayar da hankali – mahaifiyarta ta yi kokarin zub da cikinta.

Wata malamar jinya da ta ji ta tana kuka cikin bolar kayayyakin asibiti ce ta cece ta. Wannan ne labarin yadda ta tsirar da kuma uwar da ta zaci cewa ta mutu.

“Na girma da sanin cewa ni bakwai ce, kuma cewa wasu ne suka raine ni,” in ji Melissa Ohden, mai shekara 41, a hirarta da BBC.

“Abin da ban sani ba shi ne akwai wani babban sirri dangane da wannan zancen. An haife ni a raye maimakon a mace kamar yadda mahaifiyata ta so.”

A shekarar 1977, a cikin wani asibiti a jihar Iowa ta Amurka, uwar Melissa mai shekara 19 ta zub da ciki ta hanyar amfani da wani sinadari mai guba cikin kwana biyar.

  • South Korea ta hana zubda cikin ‘ya mace
  • Mata-maza za su iya aure har da haihuwa – Sheikh Daurawa

An haife ta bayan an shafe wata takwas ana rainon cikinta, kuma nauyinta bai wuce kilo 1.3 ba, an kuma ajiye Melissa cikin tarkacen kayayyakin asibiti.

Ta kasance cikin wannan halin har zuwa lokacin da wata malamar jinya ta ji kukanta mai rauni da kuma motsinta.

An garzaya da Melissa zuwa bangaren kulawa na musamman a asibiti, inda – duk da kalubalen da ta fuskanta – ta samu ta tsira.

Likitoci sun yi tunanin cewa za ta makance, kuma a wani lokaci sun yi imanin cewar tana da wata matsala ta zuciya da ka iya kashe ta.

Amma ta yi rayuwa mai cike da koshin lafiya a hannun wasu ma’aurata da suka raine ta.

“Abu ne mai ban mamaki”, in ji Melissa.

Melissa Ohden as a babyHakkin mallakar hotoMELISSA OHDEN
Image captionLikitoci sun yi tunanin cewar Melissa za ta kasance da matsaloli na lafiya da za su dade da ita

Melissa – wadda ta rubuta wani littafi game da abubuwan da ta fuskanta – ta ce ta gano cewa ta tsira daga yunkurin zub da ciki ne a lokacin da ‘yar gidan da suke rainonta ta fada mata bisa kuskure a lokacin da suke wata takaddama.

‘Yar gidan ta yi ihun cewa: “Kin sani Melissa, a kalla dai iyayena da suka haife ni suna sona”.

Da farko Melissa ta kidime, amma da ta fara ganewa – ta zauna da iyayen da suka raine ta – wannan ya jawo mata tabarbarewar lafiyar kwakwalwa.

“Na jiye wa kaina takaicin da na ji,” kamar yadda ta yi bayani. “Wuri ne mai cike da kadaici.

“Na samu matsalar cin abinci, na yi fama da yawan shan barasa. Ban so in kasance kaina ba.”

Melissa Ohden and her sisterHakkin mallakar hotoMELISSA OHDEN
Image captionMelissa tare da ‘yar uwarta

Radadin ya ci gaba da karuwa, har zuwa bayan shekara biyar – lokacin tana da shekara 19 – ta yanke shawarar neman uwar da ta zub da cikinta.

Wani mataki ne da ya dauke ta sama da shekara 10, amma daga baya ta same ta – kuma ta gano gaskiyar da ta gigita ta.

“Sirri ma fi girma a gaskiya shi ne uwata ta shafe sama da shekara 30 ta rayuwarta da imanin cewa na mutu a waccar ranar a asibitin.

“Ba a gaya mata na tsira ba. An boye mata,” in ji Melissa.

“An ajiye ni ga wadanda za su dauke ni ba tare da saninta ba.

“Ba ta sani ba ko namiji ne ko kuma mace ta haifa.”

Wannan ne ya sa a lokacin da suka fara haduwa da juna, shekara uku bayan sun fara tura wa juna sakon imel, “nadamar” da ta gani a idon uwarta ta ja hankalin Melissa matuka, wadda ta ce ta ci gaba da damunta na tsawon lokaci.

Ba ta iya siffanta yadda suka fara haduwa ba.

Melissa Ohden
Image captionMelissa tana kasa da shekara 20 ne a lokacin da ta gane gaskiya.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *