Kotun ICC ta wanke Jean-Pierre Bemba

Jean-Pierre BembaHakkin mallakar hotoAFP
Image captionA shekara ta 2016 kotu ta yanke hukunci shekara 18 akan Jean-Pierre Bemba

Sashin daukaka kara a kotun hukunta manyan laifufuka ICC da ke Hague, ya wanke Jean-Pierre Bemba daga hukuncin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.

Mista Bemba tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo ne kuma tsohon madugun ‘yan tawayen kasar.

Alkalan kotun ICC sun ce babu hujjar daura laifin kashe-kashe da fyade da aka aikata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya akan Bemba.

Mai Shara’a Christine Van ta ce da rinjaye sashin daukaka kara ya gano akwai kura-kurai a shara’ar farko da aka yi wa Mista Bemba, kuma kamar yadda sashi na 28 ya tanadar, babu wata hujjar ci gaba da tsare Bemba akan laifin da dakarun MLC suk aikata a Afirka ta Tsakiya.

  • Kotun ICC za ta yankewa Bemba hukunci
  • Bemba zai sha daurin shekara 18
  • Congo: ICC ta samu tsohon shugaba da laifi

Hukuncin dai koma baya ne ga ICC–idan aka yi la’akari da cewa shari’ar na daga cikin kalilan da ta sami nasara akai tun kafa ta a shekara ta 2002.

Wani mai magana da yawun Gwamnati ya ce Mista Bemba–wanda yanzu ya kai shekara 10 a gidan yari–na da ‘yanci komawa gida idan an sako shi.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *