Kalaman Obasanjo: Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake – Lai Mohammed

Buhari da ObasanjoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionObasanjo ya marawa Buhari baya a zaben 2015

Gwamnatin Buhari ta ce aikin gyaran barnar da PDP ta yi ne ta sa a gaba, ba zargin da ba shi da tushe ba.

A cikin sanarwar da ya fitar domin mayar da martani bayan Obasanjo ya zargi gwamnatin Buhari da kokarin kame shi, Ministan watsa labarai Lai Mohammed ya ce gwamnatinsu ba za ta bata lokacinta ba domin kokarin tozarta wani ba, ko kuma damuwa da wani zargin da ba shi da tushe.

A ranar Juma’a ne tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fitar da sanarwa yana zargin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kokarin kama shi.

Mista Obasanjo ya ce gwanatin Buhari na tattara shaidun boge domin ta daure shi saboda sukar da yake wa shugaban, inda ya ce rayuwarsa na cikin hatsari domin an kwarmata ma sa cewa yana cikin jerin sunayen mutanen da ake farauta.

A martanin da ya mayar, Lai Mohammed ya ce “gwamnatin Buhari ba za ta damu da wasu zarge-zargen da ba su da ma’ana ba, daga ko wane bangare da nufin karkatar da hankalinta ga ayyukan da ta ke.”

Ya kara da cewa: “wadanda ke da kashi a jiki ne ya kamata su ji tsoro, marar laifi ba zai damu da wani bincike ba, a zahiri ko a mafarki”.

“Hankalin gwamnati ya karkata ne ga kokarin gyara barnar da PDP ta yi a shekaru 16 kamar yadda ta fi mayar da hankali ga ci gaba da gina nasarorin da ta samu a shekaru uku”

“Wannan gwamnatin ba za taba karkata ga tozarta ‘yan kasa marar laifi ba, wannan ba tsarin shugaba Buhari ba ne da kuma gwamnatinsa. Masu laifi ne kawai za su damu,” in ji Lai Mohammed.

Ministan ya kuma ce gwamnatinsu na mutunta tsarin mulkin dimokradiya da ‘yancin albarkacin baki, amma sun fahimci cewa wadanda a lokacinsu suka yi watsi da dokokin to zai ma su wahala.

Takun saka ya zafafa tsakanin shugabannin biyu tun bayan da Mista Obasanjo, wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, ya yi Allah-wadai da yadda yake gudanar da mulki, sannan ya ce bai cancanci a sake zabarsa ba a zaben 2019.

A ‘yan kwanaki ne shi kuma Buhari ya zargi gwamnatin Obasanjo, wanda ya mulki kasar a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007, da “kashe dubban daloli kan wutar lantarki ba tare da an ga wutar a kasa ba”. Obasanjo ya musanta wannan zargi.

Abin da sanarwar Obasanjo ta kunsa

Sanarwar ta ce wasu majiyoyin tsaro sun yi zargin cewa Mista Obasanjo na cikin jerin sunayen mutanen da suke farauta, kuma rayuwarsa na cikin hadari.

“A cewar majiyoyin, yawancin jami’an tsaron suna kusa da gwamnati, kuma a kullum suna kokarin bin hanyoyin da za su iya kawar da ‘yancin da tsohon shugaban yake da shi domin kama shi da laifi.”

Sanarwar ta kara da cewa: “Haka kawai ba za mu ba wadannan rahotannin muhimmaci ba, amma saboda yawancin wadanda suka kwarmata bayanan ba su saba bayar da bayanan karya ba.”

“Wannan gwamnati tana nuna ba ta damu ba, wani lokaci tana dogaro da ayyukanta, a kullum ana rasa rayuka da dukiyoyi a jihohi da dama na kasar nan”

“Yanzu muna cikin kasar da mutum mai daraja ta uku da na hudu ke fuskantar barazana daga gwamnatin da suke yi wa aiki.”

“Akwai wasu a kasar nan yanzu da ke cikin fargaba saboda ana iya farautarsu a ci mutuncinsu ko ma a kashe su kamar yadda yakin 2019 ya dauki wannan salon”

Sanarwar ta kuma ce “bayanan sun nuna abubuwa guda biyu a yanzu, na farko shi ne ana iya kwace Fasfo dinsa a daure shi har abada, domin hana shi sake yin tsokaci game da lamurran da suka shafi gwamnati da tafiyar da tattalin arziki da kuma tsaron ‘yan kasa da dukiyoyinsu.

“Abu na biyu kuma shi ne, gwamnati na son amfani da hukumar EFCC domin sake bude bincike kan ayyukan gwamnatin tsohon shugaban ta hanyar amfani da bayanai da shedu na karya.”

line

Sabanin Obasanjo da Buhari

ObasanjoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionObasanjo ya mulki Najeriya a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007
 • Obasanjo ya goyi bayan Buhari a zaben 2015
 • A watan Janairun 2018 ne Obasanjo ya bukaci Buhari kada ya nemi wa’adin shugabanci na biyu
 • Obasanjo ya ce Buhari ya gaza inda ya bukaci ya sauka cikin mutunci bayan wa’adinsa na farko
 • A martaninta, gwamnatin Buhari ta ce ba za ta iya muhawara da Obasanjo ba
 • Ministan watsa labaria Lai Mohammed ya ce idon Obasanjo ya rufe ga nasarorin gwamnatin Buhari
 • Buhari da Obasanjo sun hadu a taron Tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na Habasha a ranar 28 ga Janairu
 • A watan Afrilu Obasanjo ya jaddada cewa Buhari ya gaza wajen ciyar da Najeriya gaba.
 • Obasanjo ya ce bai kamata a sake zaben Buhari ba saboda gazawarsa.
 • Obasanjo ya kafa wata kungiyar siyasa bayan ya caccaki gwamnatin Buhari
 • A ranar 22 ga Mayu Buhari ya soki gwamnatin Obasanjo kan lantarki
 • Buhari ya ce wani tsohon shugaban kasa ya kashe dala biliyan 16, kuma har yanzu ba lantarki
 • Obasanjo ya mayar wa Buhari da martani a ranar 22 ga Mayu
 • Obasanjo ya ce gwamnatin Marigayi Umaru ‘Yar’adu ta kafa kwamitin bincike, kuma kwamitin ya wanke shi. BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *