Buhari na hada shaidun boge domin kama ni – Obasanjo

Obasanjo da BuhariHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA baya shugabannin biyu na dasawa da juna amma yanzu sun babe

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari na tattara shaidun boge domin ya daure shi saboda sukar da yake masa.

“Wadansu majiyoyi na tsaro sun tabbatar min da cewa gwamnati na shirin amfani da hukumar EFCC da wasu shaidun boge domin kama ni da kuma tsare ni na din-din-din,” a cewarsa.

Wannan zargi na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Mr Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya fitar a birnin Abeokuta ranar Juma’a, wadda kafafen yada labaran kasar suka wallafa.

Takun saka ya zafafa tsakanin shugabannin biyu tun bayan da Mr Obasanjo, wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, ya yi Allah-wadai da yadda yake gudanar da mulki, sannan ya ce bai cancanci a sake zabarsa ba a zaben 2019.

A ‘yan kwanaki ne shi kuma Buhari ya zargi gwamnatin Obasanjo, wanda ya mulki kasar a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007, da “kashe dubban daloli kan wutar lantarki ba tare da an ga wutar a kasa ba”. Obasanjo ya musanta wannan zargi.

Kawo yanzu babu wani martani daga fadar shugaban kasa, kuma BBC ba ta yi nasarar jin ta bakinsu ba kawo yanzu.

 • Buhari ya yi tsufa da sake tsayawa takara – Obasanjo
 • Shekara 20: Da me za ku iya tuna Sani Abacha?
 • Sau nawa Obasanjo na yi wa shugabannin kasa baki?

Abin da sanarwar ta kunsa

Sanarwar ta ce wasu majiyoyin tsaro sun yi zargin cewa Mr Obasanjo na cikin jerin sunayen mutanen da suke farauta, kuma rayuwarsa na cikin hadari.

“A cewar majiyoyin, yawancin jami’an tsaron suna kusa da gwamnati, kuma a kullum suna kokarin bin hanyoyin da za su iya kawar da ‘yancin da tsohon shugaban yake da shi domin kama shi da laifi.”

Sanarwar ta kara da cewa: “Haka kawai ba za mu ba wadannan rahotannin muhimmaci ba, amma saboda yawancin wadanda suka kwarmata bayanan ba su saba bayar da bayanan karya ba.”

“Wannan gwamnati tana nuna ba ta damu ba, wani lokaci tana dogaro da ayyukanta, a kullum ana rasa rayuka da dukiyoyi a jihohi da dama na kasar nan”

“Yanzu muna cikin kasar da mutum mai daraja ta uku da na hudu ke fuskantar barazana daga gwamnatin da suke yi wa aiki.”

“Akwai wasu a kasar nan yanzu da ke cikin fargaba saboda ana iya farautarsu a ci mutuncinsu ko ma a kashe su kamar yadda yakin 2019 ya dauki wannan salon”

Sanarwar ta kuma ce “bayanan sun nuna abubuwa guda biyu a yanzu, na farko shi ne ana iya kwace Fasfo dinsa a daure shi har abada, domin hana shi sake yin tsokaci game da lamurran da suka shafi gwamnati da tafiyar da tattalin arziki da kuma tsaron ‘yan kasa da dukiyoyinsu.

“Abu na biyu kuma shi ne, gwamnati na son amfani da hukumar EFCC domin sake bude bincike kan ayyukan gwamnatin tsohon shugaban ta hanyar amfani da bayanai da shedu na karya.”

line

Sabanin Obasanjo da Buhari

ObasanjoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionObasanjo ya mulki Najeriya a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007
 • Obasanjo ya goyi bayan Buhari a zaben 2015
 • A watan Janairun 2018 ne Obasanjo ya bukaci Buhari kada ya nemi wa’adin shugabanci na biyu
 • Obasanjo ya ce Buhari ya gaza inda ya bukaci ya sauka cikin mutunci bayan wa’adinsa na farko
 • A martaninta, gwamnatin Buhari ta ce ba za ta iya muhawara da Obasanjo ba
 • Ministan watsa labaria Lai Mohammed ya ce idon Obasanjo ya rufe ga nasarorin gwamnatin Buhari
 • Buhari da Obasanjo sun hadu a taron Tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na Habasha a ranar 28 ga Janairu
 • A watan Afrilu Obasanjo ya jaddada cewa Buhari ya gaza wajen ciyar da Najeriya gaba.
 • Obasanjo ya ce bai kamata a sake zaben Buhari ba saboda gazawarsa.
 • Obasanjo ya kafa wata kungiyar siyasa bayan ya caccaki gwamnatin Buhari
 • A ranar 22 ga Mayu Buhari ya soki gwamnatin Obasanjo kan lantarki
 • Buhari ya ce wani tsohon shugaban kasa ya kashe dala biliyan 16, kuma har yanzu ba lantarki
 • Obasanjo ya mayar wa Buhari da martani a ranar 22 ga Mayu
 • Obasanjo ya ce gwamnatin Marigayi Umaru ‘Yar’adu ta kafa kwamitin bincike, kuma kwamitin ya wanke shi. BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *