Cutar kwalara na kara kamari a wasu jihohin Najeriya

Cutar kwalara na kara kamari a jihohin arewa maso gabashi da kuma arewa maso yammacin Najeriya

A Najeriya, cutar kwalera na ci gaba da lakume rayukan jama’a da kuma jefa wasu cikin mawuyacin hali a jihohi daban-daban na kasar.

Mutane gommai ne suka rasu sakamakon wannan cuta kawo yanzu, inda kuma ta kama mutane fiye da dubu uku galibi a jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Yobe sai kuma baya-bayan nan Kaduna.

Wasu mutane da lamarin ya shafa a garin Mubin jihar Adamawa inda ake jin nan ne abin ya fi kamari, sun shaida wa BBC cewa, shan gurbataccen ruwa da jama’ar garin Mubi suke yi ne ya janyo barkewar wannan cuta.

Mazauna garin sun ce duk da yake garinsu babban gari ne, suna fama da matsalar karancin ruwan famfo domin sha da sauran amfanin yau da kullum.

Suka ce, saboda karancin ruwan shan ne, suke amfani da ruwan rijiya, wadda kuma ba bu tabbas a tsaftarta.

  • Yadda kwalara ke yaduwa a Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Fiye da dalibai 50 sun kamu da kwalara a wata makaranta a Kaduna
  • Kwalara ‘ta kama’ ministocin Kenya

A nata bangaren, gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan watsa labaran jihar Alhaji Ahmed Sajo, wanda ya shugabanci wata tawaga zuwa garin domin ganin abin da ya faru, ya shaida wa BBC cewa, ko shakka ba bu ana samun wannan matsala a duk shekara.

Alhaji Sajo, ya ce shan gurbataccen ruwa ne ya janyo barkewar cutar a Mubi.

Kwamishinan ya ce, a yanzu asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, da kuma hukumar lafiya ta duniya WHO, sun horar da mutane wadanda za su rinka sa sinadarin chlorine mai kashe kwayoyin cuta a cikin ruwan da mutanen garin ke amfani da shi.

Alhaji Sajo, ya ce a matakin gwamnati kuma, yanzu suna kokarin samun wuraren da ke ruwa isashshe a tona manyan rijiyoyin burtsatsai don amfanin al’ummar garin.

Kuma gwamnati na kokarin gyara injinan da ke aiki a ma’aikatar samar da ruwa da ke garin, wadanda ‘yan Boko Haram suka lalata.

Kwamishinan lafiyar ya ce, sakamakon fara zuba sinadarin chlorine din, ya sa an rage kamuwa da cutar a yanzu, saboda tsaftace ruwan da aka fara.

Wannan layi ne

Karin bayani akan cutar kwalara

A kan kamu da cutar da kwalara sakamakon ta’ammali da gurbataccen ruwan sha da abinci ko kuma kazanta.

Jihohi da dama a Najeriya ne ke fama da bullar amai da gudawa inda har hukumomin lafiya na duniya suka kaddamar da riga-kafin cutar wadda suka ce za ta karade kasashe da dama na Afirka.

A farkon watan Mayu ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da dala miliyan biyu ta hannun Asusun Agaji na Najeriya, domin shawo kan cutar kwalarar da ta barke a arewa maso gabashin kasar, wadda ake tsoron idan ba a magance ta ba za ta iya shafar dubban mutane.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *