Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasara a kotu

Shugaban kasar NajeriyaHakkin mallakar hotoAFP
Image captionShugaba Muhammadu Buhari ya shafe wata da watanni a birnin Landan yana jinya a bara

Wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin cewa ba dole ba ne Shugaba Muhammadu Buhari mai shekara 75 ya bayyana yawan kudin da aka biya lokacin da ya yi jinya a Landan a bara.

Wata kungiyar farar hula mai rajin kare hakkin al’umma da samar da ababen more rayuwa ce ta shigar da kara a gaban kotu bayan da babban bankin kasar ya ki bayyana yawan kudin da aka kashe a lokacin da ya yi doguwar jinyar.

Mai sharia John Tsoho ya ce dokar ‘yancin samun bayanai ba ta bada damar bada bayani ba a batutuwan da suka shafi fitar da bayani kan wani ba tare da amincewarsa ba, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Babu wata hujja da ta nuna cewa shugaban kasa ya amince a fitar da bayani a kan rashin lafiyarsa kuma babu wata sanarwar da aka fitar game da haka” in ji alkalin.

Ya kara da cewa “Kotu ba ta amince da karar da aka shigar a gabanta ba kuma ta yi watsi da ita”.

Sau uku Shugaba Buhari ya yi balaguro zuwa Landan domin duba lafiyarsa a bara.

 • An yi fim game da kalaman Buhari kan matasa
 • Makiya na neman ganin bayan Buhari – Adesina

Kuma bai bayyana rashin lafiyarsa da yake fama da ita ba, amma ya ce “bai taba rashin lafiya irin wannan ba”.

Ga dukkan alamu ya murmure daga rashin lafyar kuma ya ce zai tsaya takarar neman wa’adi na biyu a zaben shugaban kasa da za a yi a badi.

A kwanakin baya-baya nan wani babban likita a Najeriya Osahon Enabulele ya zargi shugaban da rashin cika alkawarin da ya yi na kawo karshen zuwa kasashen waje domin neman lafiya.


Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

BuhariHakkin mallakar hotoPHOTOSHOT
Image captionWata mai goyon bayan Buhari na sumbatar hotonsa da aka manna
 • Shekararsa 76
 • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
 • Ya bayyana aniyarsa ta neman wa’adi na biyu a zaben 2019
 • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
 • An hambare shi a juyin mulki
 • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
 • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
 • Mai ladabtarwa ne – a kan sa ma’aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
 • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
 • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa.
 • BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *