An tsayar da wasan kwallon kafa don buda baki

Sports
Mouez HassenHakkin mallakar hotoTÉLÉVISION TUNISIENNE 1
Image captionA lokacin da mai tsaron gida Mouez Hassen ya fadi bayan faduwar rana, inda daga nan aka tsayar da wasan

‘Yan wasan kasar Tunisiya sun samu wata dabarar yin buda-baki a lokacin wasannin sada zumunta na shirye-shiryen fara Gasar Cin Kofin Duniya.

A cikin wasanninsu na makon da ya gabata, mai tsaron gidan Tunisiya, Mouez Hassen, ya kwanta a kasa bayan an dawo daga hutun rabin lokaci yana mai korafin ya ji ciwo yayin da wani ma’aikacin kiwon lafiya ya shiga filin wasan.

A wasansu na farko da Portugal lokacin da ake cinsu 2-1, Hassen ya yi kamar ya ji wa kansa ciwo a minti na 58 da fara wasan, wani matakin da ya bai wa takwarorinsa damar fita wajen fili domin yin buda-baki.

Bayan sun ci dabino da shan ruwa, ‘yan wasan na arewacin Afirka sun zura kwallo daya a raga bayan minti shida da komawa wasan, inda aka tashi wasan canjaras 2-2.

Hakazalika a minti na 49 a fafatawarsu da Turkiyya ranar Asabar, Hassen ya kwanta a bayansa yayin da wadansu ‘yan wasan Tunisiya suka ruga wajen fili domin su ci abincin buda-baki.

'Yan wasan TunisiyaHakkin mallakar hotoTÉLÉVISION TUNISIENNE 1

‘Yan tawagar na Carthage sun tashi wannan wasan shi ma kunnen doki 2-2.

Daruruwan miliyoyin Musulmi daga sassan duniya suna azumi a cikin watan Ramadan.

'Yan wasan TunisiyaHakkin mallakar hotoTÉLÉVISION TUNISIENNE 1

Wata ne na da’a inda Musulmi kaurace wa ci da sha da shan sigari da kuma jima’i daga fitowar alfijir zuwa faduwar ranar.

Sai dai kuma ba dole Tunisiya ta shiga Gasar Cin Kofin Duniya da wannan dabarar ba domin za a gama azumin kafinsu fara wasansu na farko a ranar 18 ga watan Yuni.

Tunusiya tana rukunin G, inda za ta fafata da kasashen Ingila da Belgium da kuma Panama.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *