Tsoffin ‘yan sabuwar PDP sun fasa ganawa da Osinbajo

News
Bukola SarakiHakkin mallakar hotoTWITTER/SARAKI
Image captionBukola Saraki ya dade yana takun saka da shugaban rundunar ‘yan sandar kasar

Tsoffin ‘yan sabuwar PDP da suka hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, sun dakatar da ganawar da za su yi da Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo.

A ranar Litinin ne bangarorin biyu suka shirya ganawa da juna, kamar yadda aka tsara tun farko.

Wata sanarwa da Alhaji Abubakar Kawu Baraje, shugaban ‘yan PDP sabuwa ya raba wa manema labarai ta ce hankalinsu ya tashi tun bayan ganawar da suka yi da Mista Osinbajo saboda yadda fadar shugaban kasar take yi wa wadansu shugabannin majalisa bita da kulli.

A ranar Lahadi ne ‘yan sandan suka ce wasu mutane da ake tuhuma da fashin ne suka ce “Saraki ne ya ke daukar nauyinsu”, a don haka suka gayyace shi domin ya amsa tambayoyi.

Sai dai Sanata Bokola Saraki ya musanta zargin ‘yan sandan.

  • Saraki ko Kwankwaso: Wa zai iya ja da Buhari a APC?
  • APC ta sha kaye a hannun PDP a zaben jihar Oyo
  • 2019: Buhari yana da matsala a Arewa – Buba Galadima

Sai dai kawo yanzu gwamnatin Najeriya ba ta ce komai ba game da kalaman Alhaji Kawu Barajen.

“Saboda wadannan abubuwan da ke faruwa ne a cikin sa’o’i 24 ya sa bangarenmu ya janye daga tattaunawa da bangaren shugaban kasa,” a cewar Alhaji Kawu Barajen.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya dade yana takun saka da shugaban rundunar ‘yan sandar kasar.

Ana tattaunawar ne dai a wani kokarin sulhunta rashin jituwar da ke tsakanin bangarorin biyu.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *