”Yan sanda sun yi amai sun lashe kan Saraki’

Reports
Bukola SarakiHakkin mallakar hotoTWITTER/@BUKOLASARAKI

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce rundunar ‘yan sandan kasar ta ce ba ta gayyaci shi ba.

A ranar Lahadi ne ‘yan sandan suka ce wasu mutane da ake tuhuma da fashi ne suka ce “Saraki ne ya ke daukar nauyinsu,” a don haka suka gayyace shi domin ya amsa tambayoyi.

Rahotannin da suka ce ana neman Bukola Saraki game da fashin da aka yi a garin Offa na jihar Kwara sun ja hankalin mutane sosai a Najeriya.

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Saraki ya ce ya nemi dogarinsa ya karbo takardar sammacin daga rundunar ‘yan sanda domin ya je ya kare kansa.

Amma zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan ba ta ce komai ba kan janye kalaman nata da Saraki ya ce ta yi.

Sai dai kuma daga baya ya sake wallafa wani sako inda ya ce hukumar ‘yan sandan ta ce ba gayyatarsa ta yi ba, tana so ne ya mayar da martani a rubuce game da zargin da ake masa.

  • A shirye nake na amsa gayyatar ‘yan sanda – Saraki
  • Fashi da makami: ‘Yan sanda sun gayyaci Saraki

Ya ce: “Bayan sakon da na wallafa dazu, na sami wasika daga hukumar ‘yan sandan Najeriya. A yanzu ba sa bukatar in je ofishinsu, amma suna son in mayar da martani a rubuce game da zarge-zargen cikin sa’a 48 — abin da nake shirin yi.”

Gayyatar na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari a jam’iyyar APC mai mulki, inda Saraki da wasu gaggan jam’iyyar suka zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da yi musu bita da kulli, da hana su rawar gaban hantsi.

Saraki, wanda ya fito daga jihar Kwara, ya ce “Ya kamata kowa ya sani cewar babu yadda za a yi in kasance ina da alaka da fashi da makami akan mutanena.”

Ya kara da cewa: “A lokacin da aka yi fashi a garin Offa, ni ne babban jami’in gwamnati na farko da na fara zuwa wurin, kuma a fadar sarkin garin na kira Mista Ibrahim Idris, sufeto janar na ‘yan sanda, ina mai neman ya tanadi wasu shirye-shirye na tsaro kamar yadda mutanen garin suka nema.”

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *