Fashi da makami: ‘Yan sanda sun gayyaci Saraki

SarakiHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionSanata Bokola Saraki ya musanta zargin ‘yan Sandan

‘Yan sandan Najeriya sun gayyaci shugaban Majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki domin ya amsa tambayoyi game da wani bincike da suke gudanarwa kan fashi da makami.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce ta tatsi bayanai daga wasu gaggan ‘yan fashi biyar da wasu 17 da ta kama wadanda ake zargi sun yi fashi a wasu Bankuna a Offa.

Sanarwar ‘yan sandan ta ce ‘yan fashin sun fada da bakinsu cewa “su ‘yan bangar siyasa ne na shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki da kuma gwamnan Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed.”

Sai dai shugaban Majalisar dattijan Sanata Bukola Saraki da gwamnan Kwara dukkaninsu sun musanta zargin da kuma alakar su da ‘yan fashin.

Saraki ya taba cewa ‘yan sandan na kokarin bin hanyoyin duk da za su bi domin su bata ma sa suna.

An dade ana takun-saka tsakanin Majalisar Dattijai da ‘yan sandan Najeriya musamman bayan majalisar ta gayyaci Sufeton ‘yan sandan Ibrahim K. Idris amma ya ki zuwa da kansa.

  • Yadda ‘yan sanda suka tarwatsa magoya bayan Shekarau
  • Saraki ko Kwankwaso: Wa zai iya ja da Buhari a APC?

Sanarwar ‘yan sandan ta ce “‘Yan fashin sun fadi cewa su ‘yan bangar siyasa ne karkashin kungiyar matasa da ake kira Good Boy, tare da cewa suna samun tallafin kudi da makamai da motoci daga Sanata Bukola Saraki da gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed.”

‘Yan sandan sun bukaci Saraki ya kai kansa ofishinsu da ke Guzafe a Abuja domin amsa tambayoyi kan zarginsa da ‘yan fashin suka yi.

Sannan sanarwar ta kara da cewa ‘yan fashin sun fadi da bakinsu cewa su ne suka yi fashi a bankuna guda shida da ke Offa tare da kai hari a babban ofishin ‘yan sanda a garin, inda suka kwashi kudi da kuma bindigogi kirar AK47 guda 27.

‘Yan sandan sun ce mutane kimanin 33 ne ‘yan fashin suka kashe cikinsu har da mata ma su juna biyu da kuma jami’an ‘yan sanda tara.

‘Yan sandan sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike, kuma idan an kammala binciken za a gabatar da wadanda ake zargi a kotu domin a hukunta su.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *