LABARAI A TAKAICE

*Rundunar ‘yan sanda a jihar Ekiti, Najeriya ta ce dan sandan nan da ya bude wuta kan kamfen din dan takarar gwamnan APC Kayode Fayemi, ya sato hanya ne daga Ikeja Lagos inda a ka sanya shi aikin gadin bankuna.*

*Dan sandan dai ya rako wani dan siyasa ne zuwa Ekiti ba tare da izini ba inda ya aikata laifin. Yanzu haka dai an kama dan siyasar da ya dauko dan sandan inda jigon APC Opeyemi da wani mutum daya da albarushin dan sandan ya samu, na samun sauki a a sibiti.*

*Labarin farko da a ka samu shine mutumin na biyu ya riga mu gidan gaskiya. Hakanan rundunar ta ce cikin kuskure dan sandan ya bude wuta kuma a yanzu ana rike da shi a wani waje da a ke yi ma sa magani bayan dukan kawo wuka da magoya bayan APC su ka yi ma sa.*

*APC a Ekiti ta dakatar da kamfen da zargin cewa wani shiri a ka kulla na kashe Kayode Fayemi.*

*Sakataren babban taron jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Benjamin Uwajomogu ya sanar da murabus din sa daga mukamin ya na mai watsi da zargin ya yi sama da fadi da kudin kwamitin.*

*Uwajumogu ya ce ya ajiye mukamin ne bisa bukun kyashin kai don wasu bukatu na iyalin sa da kuma bunkasa APC a jihar Imo.*

*Uwajumogu ya godewa shugaban jam’iyyar John Odigie Oyegun don ba shi wannan dama da kuma ya yi fatar taro ya wanye lafiya.*

*Gwamnan Bauchi a Najeriya Muhammad Abdullahi ya zabi shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar Audu Sule Katagum ya zama mataimakin gwamnan jihar bayan murabus din tsohon mataimakin sa Nuhu Gidado.*

*Kwamishinan labaru na jihar Umar Sade ya ce gwamnan ya dau matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan batun na jihar.*

*Mako mai zuwa majalisar dokokin jihar za ta yi zama don tabbatar da wannan nadi. Tsohon mataimakin gwamnan dai Nuhu Gidado da alamu zai sake fitowa don neman tikitin takara a 2019.*

*’Yan bindiga masu fashin shanu sun sake afkawa wani kauye a jihar Zamfara inda suka kashe akalla mutum 23 a ranar juma’a.*

*’Yan bindigar sun kai harin ne a kauyen Zaloka da ke cikin karamar hukumar Anka. Bayan kisan mutane, maharan sun kuma cinnawa gidaje wuta a kauyen na Zaloka*

*Sojojin gwamnatin Yaman na nausawa cikin yankin Hodeida mai muhimmanci don kwace shi daga ‘yan tawayen Houthi ‘yan Shi’a da su ka hana zababbiyar gwamnati zama da ma yin mummunan kisan gilla ga tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh.*

*Yanzu dai sojojin na tunkarar filin saukar jiragen sama na Hodeida bayan karade gundumar Hussaeiniyya,Tahita da Baitel Faqih.*

_*Ibrahim Baba Suleiman*_
_*Jibwis Social Media*_
_*18-Ramadan-1439*_
_*03-June-2018.*_

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *