Labarin ‘yan Shi’ar da aka nema aka rasa a Pakistan

CCTV footage
Image captionTun a ranar 16 ga watan Nuwamba shekarar 2016 Naeem Haider ya bata

Wasu hotunan kyamarorin tsaro na wani masallaci ya nuna lokacin da gomman jami’an tsaro suka wuce da Naeem Haider mai shekara 30 hannunsa daure da sarka.

Wasu daga cikin jami’an tsaron sun rufe fuskokinsu, yayin da wasu ke sanye da kayan sarki.

Lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2016, kuma tun bayan wannan lokaci ba a sake jin duriyyarsa ba.

Duk da cewa an gabatar da hoton a matsayin shaida a gaban kotu, amma ‘yan sanda da jami’an leken asiri sun fada wa kotu cewa ba a hannunsu ya tsare ba.

Mista Haider na cikin ‘yan shi’ar Pakistan 140 da suka “bata,” a cikin shekara biyu da suka gabata, a cewar masu fafutuka.

Iyalan mutanen sun yi amannar cewa jami’an leken asiri ne suka kama shi.

A cikin mutum fiye da 25 da suka bata, ciki har da Naeem Haider kuma dukkanninsu mazauna Karachi ne, wanda shi ne gari mafi girma a Pakistan.

Iyalan Haider sun ce ya dawo daga garin Karbala da ke Iraki inda ya je ya yi ibada tare da matarsa mai juna biyu kafin aka tsare shi.

Tuni Uzma Haider ta haifi da namiji wanda bai taba ganin mahaifinsa ba.

Ta shaida wa BBC cewa: “Yara na tambayata, ‘Shin yaushe ne mahaifinmu zai dawo gida?’ Shin wacce irin amsa ce zan ba su ? Babu wani da ya yi man bayani a kan wurin da yake ko halin da yake ciki. Ya kamata a fada mana laifin da ake zarginsa da aikatawa.”

Uzma Haider da yaronta
Image captionYara na tambayata yaushe ne babanmu zai dawo gida? In ji matar Heidar

Sauran iyalan ‘yan shi’a da suka “bata” sun bayar da labari makamancin wannan, inda suka ce jami’an tsaro sun zo gidajensu cikin dare inda suka wuce da mazajensu.

Wasu mata sun taru suna kuka a gaban wani gida da ke unguwar ma’aikata ‘yan shi’a a garin Karachi, kuma sun fadawa BBC cewa mahukunta ba su yi bayani ba game da makomar ‘yan uwansu da ke tsare, ko kuma laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Sai dai wasu masu karfin fada a ji a cikin al’umma sun ce an fada musu cewa ana zarginsu da alaka da wata kungiyar sirri da ke Syria da ake kira the Zainabiyoun Brigade, da ake kyautata zaton cewa akwai ‘yan shi’a ‘yan Pakistan 1,000 wadanda suke fada a madadin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Naeem Haider
Image captionNaeem Haider

Hubbaren Zainab bint Ali jikanyar SAW na cikin birnin Damascus da ke Syria, kuma manufar kungiyar ita ce ta hana masu tsattsauran ra’ayin Sunni irinsu IS lalata wurin, wadanda suka yi amannar cewa wurare irin wannan sun sabawa koyarwar adinin musulunci.

An yi amannar cewa mayakan Zainabiyoun sun yi fada a fagen daga da dama a Syria ciki har da Aleppo.

Sai dai ba sa cikin jerin sunnayen kungiyoyin da ma’aikatar cikin gida ta Pakistan ta haramta ba, kuma ba a taba tuhumar wani daga cikin mazan da suka bace da laifi ba.

  • ‘Yan sanda na amfani da karfi a kan ‘yan shi’a – Amnesty

Rashid Rizvi shi ne jagoran kwamitin ‘yan shi’a da suka bace a Karachi.

Ya jogoranci jerin zanga-zangar da aka yi a cikin garin inda aka nemi ko a saki mutanen, ko kuma a gurfanar da su gaban kotu.

Ya ce an tsare mutanen ne bayan da suka kai ziyara yankin Gabas ta Tsakiya domin yin ibada.

Ya shaida wa BBC cewa: “Wakilan wasu cibiyoyin gwamnati sun zo wurina,” wato yana nufin jami’an leken asiri.

“Sun yi kokarin shawo kanmu a kan mu kawo karshen zanga-zangar da mu ke yi … Na tambaye su ‘Shin mene ne dalilin da ya sa suka kama wadanan mutane?’ Sai suka ce, ‘Muna kyautata zaton cewa sun je Syria domin su yi fada da kungiyar Daesh (IS) da al-Qaeda.’

“Sai na ce, ‘ Idan haka lamarin yake to ya kamata su gurfanar da su gaban shari’a… shin me yasa aka nada alkalai kuma aka kafa kotuna?”

Wannan layi ne

Jami’an tsaron Pakistan ba su ce komai ba ga bukatar da BBC ta shigar gabansu domin su yi bayani.

“Mutanen da suka bata na cikin batutuwa masu sosa rai a Pakistan”.

A cewar wata kididiga ta gwamnati, mutum fiye da 1,500 ne suka bata wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

A cikin wadanda suka bata har da mayakan ‘yan sunni masu ikirarin jihadi, da kuma mayaka masu fafutukar kare hakkin kabilunsu da kuma masu sassaucin ra’ayi da ke sukar rundunar sojin Pakistan.

Hukumomi a Pakistan sun ce ana dora alhakin bacewar mutane a kan jami’an tsaron kasar ba tare da wata hujja ba. Kuma ana ruruta yawan wadanda suka bata.

Sai dai daga bisani an saki wasu daga cikin maza ‘yan shi a da aka kama.

Samar Abbas
Image captionSamar Abbas, wani mai fafutuka da aka tsare fiye da shekara guda
Wasu mazauna garin Yarmouk sun koma bayan da aka kwato wurin daga hannun IS a ranar , 24 ga watan Mayu 2018Hakkin mallakar hotoEPA
Image captionAn shiga shekara ta bakwai tun bayan barkewar yakin basasa a Syria
Shamimara na kuka lokacin da take magana kan danta
Image captionShamimara ta shafe shekara guda ba ta sake jin duriyar danta ba.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *