An sake kashe mutum 23 a Zamfara

Taswirar Zamfara

‘Yan bindiga masu fashin shanu sun sake afkawa wani kauye a jihar Zamfara inda suka kashe akalla mutum 23 a ranar juma’a.

‘Yan bindigar sun kai harin ne a kauyen Zaloka da ke cikin karamar hukumar Anka.

Bayan kisan mutane, maharan sun kuma cinnawa gidaje wuta a kauyen na Zaloka.

Shugaban karamar hukumar Anka Alhaji Mustafa Muhammad Anka wanda ya tabbatar wa da BBC da faruwar lamarin, ya ce har an yi jana’izar mutanen 23 da maharan suka kashe.

Ya kuma ce akwai sakon wasika da barayin suka bari bayan sun kai harin, amma ba tare da ya bayyana abin da wasikar ta kunsa ba.

Garin Zaloka dai na kusa da kauyen Bawar Daji inda wasu mahara suka yi wa akalla mutum 28 yankan rago a watan Maris.

  • Me ya sa babu wanda ya damu da rikicin Zamfara?
  • An kashe mutum 27 a Zamfara

Wani mazauni yankin, ya shaida wa BBC cewa a ranar juma’a da maharan suka kai hari a Zaloka, daga Bawar daji suna jin karar harbin bindiga.

Jihar Zamfara ta dade tana fuskantar hare-hare daga mutanen da ake zargi ‘yan fashi ne da barayin shanu.

Kuma Zamfara na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa.

Masu sharhi kan sha’anin tsaro da ma ‘yan kasar na ganin matakan da ake dauka ba su yi tasirin hana hare-haren ba da ake kai wa kusan a kullum a Jihar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *