Shekara uku na mulkin Buhari ‘ba yabo ba fallasa’

Shugaban Najeirya muhammadu BuhariHakkin mallakar hotoPRESIDENCY
Image captionShugaba Buhari zai nemi wa’adin shugabanci na biyu

Shin farin jininsa ya ragu ko ya karu? yayin da wasu ‘yan kasar ke bayyana shekaru uku na mulkinsa da cewa ‘ba yabo ba fallasa’.

A ranar 29 ga watan Mayun 2018 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekaru uku akan mulki bayan rantsar da shi a 2015.

A cikin jawabinsa a ranar dimokuradiya da gwamnatinsa ke cika shekaru uku, shugaban ya ce duk da sun fuskanci kalubale, amma gwamnatinsa ta samu nasarori a fannoni uku da ta sa gaba – wato tsaro da yaki da rashawa da kuma tattalin arziki.

Sannan Shugaban ya ce an samu ci gaba ta fuskar samar da hasken wutar lantarki, yana mai cewa “an rage amfani da janareto saboda wadatuwar lantarkin.”

Sai dai ‘yan Najeriya sun ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da cikar gwamnatinsa shekaru uku.

Mutane da dama ne suka bayyana ra’ayoyinsu tare da tafka muhawara a shafin Facebook na BBC Hausagame da shekaru uku na mulkin Buhari.

Wasu sun yabi gwamnatin, yayin da wasu kuma ke cewa har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, musamman ga gwamnatin da aka zaba domin kawo sauyi a Najeriya.

Ra'ayoyin FacebookHakkin mallakar hotoFACEBOOK

Gwamnatin Buhari dai ta samu nasarar karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso yammaci.

Amma wasu ‘yan kasar na ganin yawan kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake samu musamman a Zamfara da wasu jihohi wani koma-baya ne ga gwamnatin Buhari.

Tun kafin a zabe shi, shugaban ke nanata cewa tabarbarewar tsaro ne babban mihimmin abun da zai magance.

Amma baya ga karya lagon Boko Haram da gwamnatindsa ta yi, har yanzu ana ci gaba da kisan mutane a Zamfara da Kaduna da kuma wasu jihohin da ke fama da rikicin makiyaya da manoma.

  • Kalaman Buhari kan wutar lantarki sun jawo ce-ce-ku-ce
  • Abubuwa uku da suka sa Buhari neman wa’adi na biyu

Ko da yake a cikin jawabinsa, shugaban ya bayyana damuwa da yawaitar kashe-kashen, tare da yi wa ‘yan kasa alkawalin cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen matsalar.

Wani batu kuma da ke ciwa ‘yan kasar tuwo a kwarya shi ne yadda rayuwa ta kara yin tsada a zamanin mulkin na Buhari.

Ko da yake shugaban ya karbi mulki a lokacin da farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya.

Amma wasu na ganin kudaden da gwamnatinsa ta kwato da kuma kudaden ajiyar da aka samu sun isa ace talakawan kasar sun ga sauyi a gwamnatin.

Ra'ayoyin FacebookHakkin mallakar hotoFACEBOOK

Gwamnatin Buhari wadda ta yi karin farashin litar fetir daga Naira 97 zuwa Naira 145, ta ce tana kokarin farfado da tabarbarewar tattalin arzikin da ta gada ne daga gwamnatin da ta gabata.

A cikin jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce an samu bunkasar tattalin arziki karkashin wani shirin gwamnatinsa na farfado da tattalin arzikin daga shekarar 2017 zuwa 2020.

Ya ce wani binciken da gwamnati ta gudanar a kwanan nan a fannoni uku na tattalin arziki, da suka hada da noma da sufuri da lantarki da Gas, ya yi hasashen za a samu yawaitar masu zuba jari tare da samar da ayyukan yi sama da 500,000 zuwa 2020.

Ya kara da cewa an dauki matasa aiki 200,000 a shirin N-Power, kuma tuni aka zabi 300,000 da za a sake dauka aiki.

Shugaban ya kuma ce asusun ajiyar Najeriya ya karu zuwa dala biliyan 47.5 a watan Mayu daga dala biliyan 29.6 a 2015.

Ya ce asusun bai-daya na TSA ya taimaka wa gwamnatinsa wajen adana biliyoyin daloli inda ya ce an ajiye dala biliyan 200 na daga ma’aikatan bogi da aka gano a ma’aikatun gwamnati.

A kwanakin baya ne dai, Shugaban na Najeriya ya bayyana aniyarsa ta sake neman wa’adin shugabanci na biyu a zabe mai zuwa.

Sai dai wasu masana na ganin akwai babban kalubale a gabansa ganin yadda wasu da dama ciki har da ‘yan jam’iyarsa suka dawo daga rakiyar gwamnatinsa.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *