Ministan Buhari ya ajiye aikinsa

News
Kayode FayemiHakkin mallakar hotoFACEBOOK/KAYODEFAYEMI
Image captionMista Fayemi ya taba kasancewa gwamnan Ekiti tsakanin shekarun 2010 zuwa 2014

Ministan Ma’adanan Najeriya, Kayode Fayemi ya mika wa Shugaba Muhammadu Buhari takardar ajiye aikinsa, kamar yadda wani na kusa da shugaban ya shaida wa BBC.

Jami’in gwamnatin wanda ya bukaci mu sakaya sunansa ya ce Mista Fayemi ya yi hakan ne a cikin makonni da suka wuce saboda yana neman gwamna a jiharsa ta Ekiti.

Ya ce shugaban kasar ya karbi takardar, amma bai bayyana amince da murabus din nasa ba tukuna.

Minsitan wanda ya taba zama gwamna a jiharsa ta Ekiti, shi ne dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a zaben da za a yi a watan Yulin bana a jihar.

  • Kwankwasiyya ta gudanar da zaben shugabannin ‘APC’ a Kano
  • Zaben shugabannin APC ‘ya bar baya da kura’

Mista Fayemi zai fafata ne da Farfesa Olusola Kolapo Eleka na jam’iyyar PDP wadda ita ce take mulkin jihar a halin yanzu.

Zaben zai iya zama zakaran gwajin dafi saboda yadda kasar za ta gudanar da babban zabe a shekarar 2019.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *