Karin albashi ba zai samu ba a Najeriya a Satumba – Gwamnati

Uncategorized
ATM NajeriyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Gwamnatin Najeriya ta ce karin mafi karancin albashi ga ma’aikata ba zai samu ba a watan Satumba kamar yadda aka ruwaito tun da farko.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya ambato Ministan kwadago da Ayyukan yi Sanata Chris Ngige, yana cewa karin albashin ba zai samu ba saboda sai a karshen watan Satumba kwamitin da aka kafa ake sa ran zai kammala aikinsa.

Mista Ngige ya ce bayan kwamitin ya gabatar da rahotonsa, sai gwamnati ta duba ta tantance kafin ta amince, daga nan sai ta tura a majalisa.

Sannan ministan ya ce batun iya biyan albashin, shi ne abu muhimmi game da karin albashin.

Ya ce aikin kwamitin ya shafi hadin kan dukkanin bangarori da suka hada da jihohi da kuma kamfanoni masu zaman kansu tare da saurarorin ra’ayoyin jama’a a fadin kasar.

  • An yi fim game da kalaman Buhari kan matasa

Da gaske ne matasan Najeriya na zaman kashe wando?

An dade ‘yan Najeriya na neman karin albashi daga mafi karancin kudin da ake biyan ma’aikaci na naira 18,000, a yayin da rayuwa ke ci gaba da tsada a kasar.

Mista Ngige ya ce akwai bambanci tsakanin jihohi da dama kan adadin kudaden albashi mafi karanci da suka ce za su iya biya a wata, kuma bambancin ya shafi daga Naira 22,000 zuwa Naira 58,000.

Gwamnatin shugaba Buhari dai ta yi alkawalin karin albashin bayan shawara da kwamitin da aka kafa a shekarar 2016 ya bayar domin gano yadda za a rage radadin tasirin karin kudin mai kan talakawa.

Kwamitin wanda ya hada da gwamnoni da shugabannin ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki, ana fatar zai cimma matsaya kan albashi mafi karanci da ya kamata a biya ma’aikaci a Najeriya.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *