An yanke wa tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame daurin shekara 14

Reports
Tsohon gwamnan jihar kotu a cikin kotu da aka yanke masa hukunciHakkin mallakar hotoDAILY TRUST
Image captionRev Jolly Nyame lokacin zaman kotun

Wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan kaso bayan ta same shi da laifin yin sama da fadi da kudi da yawansu ya kai naira miliyan 250.

Kotun ta samu Mista Nyame da laifi a tuhumce-tuhumce 27 daga cikin 41 da hukumar EFCC ta gabatar a gabanta.

Hukumar EFCC na tuhumar shi da yin almundana da kudi fiye da naira biliyan daya lokacin da ya rike da mukamin gwamnan jihar Taraba daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Alkalin kotun Mai shari’a Adebukola Banjoko ya yanke wa tsohon gwamnan hukuncin daurin shekara 14.

Wato an yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai da biyar da kuma biyu a gidan kaso bayan ta same tsohon gwamnan da laifin karbar hanci da rashawa.

Alaklin kotun ya ce ba a amince masa ya biya tara ba.

  • Kun san shugabannin Afirka da aka gurfanar a kotu?
  • An gurfanar da Sheikh Zakzaky a gaban kotu a Kaduna

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da wata kotu ta ke samun tsohon gwamna da laifin aikata almundahana ba.

A watan Mayu na shekarar 2017 wata kotu ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Adamawa James Ngilari daurin shekara biyar a gidan yari, bayan ta same shi da laifin aikata rashawa.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Sai dai wasu na zargin gwamnatin kasar da tuhumar wadanda suka rike mukamai a lokacin da jam’iyyar adawa ta PDP take mulki.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *