An ci tarar wani yaro naira biliyan 12 saboda ya tada gobarar daji

Wani alkali ya umarci wani yaro ya biya fiye da dala miliyan 36 (£27m) bayan ya amince shi ne ya tada wata mummunar gobarar da ta kwashe tsawon watanni tana ci a jihar Oregon a kasar Amurka.

Alkalin Kotun Jihar Hood River John Olson ya yanke hukuncin cewa dole sai yaron ya rubuta wasikar neman gafara ga mutane 152 wadanda suka makale a hanyan lokacin da gobarar take ci.

Gobarar wadda aka wa lakabi da Eagle Creek ta rika ci har tsawon kusan watanni uku a gundumar Columbia River Gorge, yayin da ta cinye gidaje da yawa.

Lauyan yaron ya bayyana adadin da “ba daidai ba” da wani abu na”rashin tunani”.

A watan Fabrairun, yaro mai shekara 15 – wanda ba a ambaci sunan shi ba lokacin zaman kotun- ya amince cewa ya jefa wani abin wasan wuta a ranar 2 ga Satumba 2017 cikin wani busashen rami da ke Eagle Creek Canyon – kimanin mil 50 (80km) daga Portland.

Abin da ya yi ne ya jawo gobara wanda ta ci Eka 48,000, kuma ‘yan kashe gobara suka kashe kimanin $18m wurin kashe gobarar.

An yanke masa hukuncin je ka gyara halinka har tsawon shekara biyar, inda zai yi aikin al’umma na tsawon sa’a 1,920 a wani daji da ke kasar Amurka.

Kotun ta amince da cewa yaron ba zai iya biya kudin da aka ci shi tara ba tashi guda.

The Hood County CourthouseHakkin mallakar hotoCBS
firefighters in OregonHakkin mallakar hotoWIKIMEDIA COMMONS.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *