An cire kullin hodar ibilis 106 a cikin wata mata a Indiya

News
Kwayar hodar IbilisHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image caption‘Yan sanda na farautar wani dan Najeriya wanda shi ne matar za ta mika wa kwayar

‘Yan sanda a Indiya sun ce sun yi nasara wajan cire kwayoyin hodar ibilis 106 daga cikin wata mata wadda ake zargi da kokarin shigar da kwayar ta haramtaciyyar cikin kasar.

An kama matar mai hekara 25 wadda bakuwa ce, a filin jirgin saman kasar da ke Indiya a Delhi, a ranar 14 ga watan Mayu bayan da wani ya tsegunta wa hukumomi, a cewar ‘yan sanda.

Rahotanni sun ce sai da ta yi mako guda a asibiti inda ta rika karbar magani, domin ta murmure daga kwayar hodar ibilis din da ta hadiya.

An yi kiyasin cewa kudin hodar ibilis din da ta sha ya kai rupees miliyan 50 kwatankwacin dala dubu 734.

‘Yan sanda sun yi amannar cewa matar ta hadiye kwayar ce a garin Sau Paulo, da ke Brazil, kuma an ba ta umurnin mika hodar ibilis din ga wani dan Najeriya da ke Delhi.

  • Mahaukaciyar guguwa ta hallaka mutum 100 a Indiya
  • Fitattun jaruman Indiya da suka auri junansu

Jami’ian hukumar yaki da masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi ta kasar sun fadawa jaridar Hindustan Times cewa; “ba su taba samun kwayar hodar ibilis mai yawa irin wannan ba” da aka cire daga cikin bil adama .

Sun kara da cewa hodar ibilis din da suka kwace mai inganci ce, wadda da aka samo daga Colombia, ba kamar sauran kwayoyin hodar ibilis da ake sayarwa a farashi mai rahusa ba, wadanda su ne aka fi kwacewa a mafi yawan lokuta.

‘Yan sanda na farautar wani dan Najeriya wanda shi ne matar za ta mika wa kwayar.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.