Me ya kamata a kauracewa a shafukan sada zumunta lokacin Ramadan?

Shafukan sada zumunta
Image captionShafukan sada zumunta na ci gaba da karbuwa a wajen Musulmi

Shafukan sada zumunta da muhawara na zamani wasu hanyoyi ne da al’umma ke amfani da su domin cimma bukatu daban-daban: wasu na neman ilimi, wasu kasuwanci, wasu kuwa na yin amfani da su ne domin watsa labaran karya da kuma cin zarafin jama’a.

Mutanen da suka samar da wadannan shafuka irinsu Facebook da Twitter da WhatsApp da Instagram da makamantan su sun sanya sharuddan amfani da su, cikinsu har da hana cin zarafin wani ko wasu, hana sanya hotunan batsa ko yin kalaman batanci da na batsa da dai sauransu.

Da ma dai tsarin zamantakewar Musulmi, wanda akasari addini ke jan linzaminsa, ya sanya sharuddan zaman tare.

Addinin Musulunci yana gaba-gaba wajen tabbatar da ‘yancin dan adam da kuma tsawatarwa kan abubuwan da ba su dace ba, don haka ne malamai ke kara yin kira ga masu amfani da shafukan sada zumunta su kiyaye dokokin addinin a lokacin da suke yin amfani da shafukan.

Mun tattauna da Malam Musa Sani, limamin daya daga cikin masallatan rukunin gidaje na Efab da ke Abuja, babban birnin Najeriya, kuma ya yi mana karin bayani:

Ƙarya

Watan azumiHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionWatan azumi lokaci ne da Musulmi ke dagewa wajen yin addu’o’i

Ƙarya na cikin manyan abubuwan da addinin Musulunci ke ƙyamar su. Ayoyi da dama a cikin Al-Ƙur’ani mai tsarki sun yi gargaɗi a kan karya, inda suke bayyana irin azabar da Allah ya tanadar wa maƙaryata.

Kazalika, hadisai da dama sun bayyana makaryata a matsayin mutanen da ba a bukatar azuminsu.

Misali, wani hadisi da Abu Huraira ya rawaito ya ambato Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “Duk mutumin da bai daina karya ba, Allah ba ya bukatar sa da ya daina cin abinci ko shan abin sha (wato Allah ba zai karbi azuminsa ba.)”.

Haka kuma wani hadisin na cewa, “Na hore ku da ku guji yin karya, domin mai yin karya za a rubuta sunansa a matsayin makaryaci.”

Da alama masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani da dama ba sa yin la’akari da irin wannan hadisi a lokutan azumi, ganin yadda suke watsa labarai na karya.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *