Ana jimamin mutuwar jarumar Nollywood Aisha Abimbola

Aisha AmbiolaHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/RONKEODUNSANYA

Ana ci gaba da jimamin mutuwar jarumar fina-finan Nollywood Aisha Abimbola a wani asibiti da ke kasar Canada ranar Laraba.

Marigayiyar wadda Musulma ce, ta fara yin fice ne a fim din Omege Campus na harshen Yarbanci a shekarar 2001.

Sai dai har yanzu ba a san dalilin mutuwarta ba daga iyalanta.

‘Yar wasan fina-finan Nollywood Bisola Badmus ce ta fara bayyana labarin mutuwarta a shafinta na Instagram.

Daga nan ne sai sauran abokan sana’arta suka fara bayyana sakon ta’aziyyarsu kamar haka:

Jaruma Ronke Odusanya, wadda aka fi sani da Flakky Ididowo ta ce “ta dimauta” bayan samun labarin mutuwar.

Jaruma Opeyemi Aiyeola ta ce mutuwar Aisha abu “mai wuyar daukar dangana.”

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *