Yau Litinin Shugaba Buhari Zai Ziyarci Jihar Jigawa

News

Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori

Shirye shirye sun kammala na ziyarar aiki ta yini biyu da shugaban kasa Muhammad Buhari zai kawo jihar Jigawa a yau Litinin.

A sanarwar daga sashen karbar baki na gidan gwamnati ta bayar tace ana sa ran shugaban kasa zai sauka a filin jirgin saman Dutse da misalin karfe goma na safe inda zai wuce zuwa garin Auyo domin kaddamar da aikin noman rani.

Kana daga bisani ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje a fadarsa.

Shugaban zai kuma bude aikin hanyar Tasheguwa zuwa Guri da kuma Guri zuwa Abunabo.

Daga bisani shugaban kasa zai dawo Birnin jiha Dutse inda zai kai ziyarar ban girma ga mai martaba sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi .

Sannan shugaban zai ziyarci unguwar Dasina inda zai bude tashar bada ruwansha mai aiki da hasken rana kana daga bisani a gudanar da taron masu ruwa da tsaki da kuma liyafar cin abinchi a gidan gwamnati.

A rana ta biyu ana sa ran shugaban zai kaddamar da baje kolin kayayyakin amfanin gona, sai kuma gangamin da magoya bayan jamiyyar APC suka shirya masa a filin taro na Mallam Aminu Kano dake birnin Dutse.

Bayan kammala wadannan aiyukan ne shugaban kasa zai bar Dutse zuwa Birnin tarayya Abuja.

@Rariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *