Ana Shirin Tsige Kakakin Majalisar Jihar Kano

 

…jami’an tsaro sun yi wa majalisar kawanya

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa ‘yan majalisun jihar na shirin tsige kakakinsu, Honarabul Abdullahi Yusuf Ata.

Majiyar ta rawaito cewa tuni kimanin membobin majalisar su 21 suka rattaba hannu kan nuna goyon bayan an tsige Kakakin.

Majiyar ta kara da cewa rashin cancanta da shugabanci na daga cikin dalilan membobin na tsige kakakin nasu.

Rahotanni sun bayyana cewa a safiyar yau Litinin jami’an tsaro na ‘yan sanda sun yi wa majalisar kawanya, don gudun ko ta kwana.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *