Yadda Likitoci Ke Wasa Da Rayukan Jama’an Domin Biyan Bukatun Kansu

News

 

Daga Imam A. Saleh

Lillahi warasulihi ya kamata likitoci daku kanku ma’aikatan asibitoci da kuke yajin aikin jin dadi ku kara jin tsoron Allah akan wanda kuke da shi, a ce yanzu an zo wani lokaci da za ku dinga amfani da rayukan jama’a da lafiyar su a matsayin makamin neman biyan bukatun kashin kanku na duniya?

Tsabagen rashin tausayi irin na “wasun” bafa albashi ne ba’a biya ko kuma ba’a baku akan lokacj ba, a’ah, illa dai wasu kudaden kunji-kunji, amma akansu kawai saiku kanne ido gaba gadi ku kada kai ai wai ku kun tsunduma yajin aiki, marasa lafiyar dake kwance a gadon asibitin ma ku tattara inaku-Inaku kuce ai wai bazaku ceci rayukan su ba koda suna kan gargarar mutuwa.

Kowa ya san a tsarin aikin gwamnati a Nijeriya ku din nan kuna sahun gaba wajen daukar albashi mafi maiko, amma abin kaico, sai gashi a lokuta da dama kukan zama ciki mai manta kyautar jiya, rannan ma ji nayi kunce kun tafi yajin aiki wai saboda babu kayan aiki a asibitoci, Toh mezai hana kuyi aiki da wadanda kuke dasu tunda dama Najeriya ba kamar inda kuke guduwa ku tafi ba ce wato Engila da Turai.

Ai na dauka maganar da kukeyi ta cewa aikin likitanci na tallafawa jama’a ne gaskiya ne, ashshe “wasu” daga cikin ku na neman arziki suke daukar sa, harna zuciyar su tayi kekashewar da suna ji suna gani zasu je gida su kwanta da sunan yajin aiki alhalin sun bar marasa lafiyar su dake bukatar daukin su can a gadon asibiti rai a hannun Allah.

Kuma babbar barazanar ma itace bama fa tsakani da Allah kuke shiga yajin aikin nan ba, yawancin ku kuna da asibitocin ku na kashin kanku, wadanda kuma matsawar na gwamnati suna aiki toh fa nakun nan zasuyi bamdaro suki samun kwastomomi, toh me zakuyi a dinga zuwa naku ?..sai kuke yanke shawarar tafiya yajin aiki domin in kukayi hakan babu yadda mutane zasuyi dole sai dai suje naku din nan, daga nan kuma shikenan ku kasuwa ta bude muku.

A wasu asibitocin gwamnatin ma abin kunya shine ansha kama wasu daga cikin ku suna sace kayan gwamnati suna kaiwa asibitocin su domin su karawa miyar su zaki.

Wallahi shi yasa ni run a Pramare in ana muhawara (Debate) akan wanda yafi muhimmancj tsakanin likita da makamin makaranta nake cewa Malami yafi.

Allah sarki Makamin Makaranta, shi duk da dubu 18 dibda ake biyan sa a wata bai rains ba yana cigaba da yin hidimar sa kuma shi bata fashion ballantana ace yaci haramun baya makara ballantana ace yayi dungushe, baya asha ruwan tsuntsaye ballantana ace bata kishin al’umma.

@Rariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *