Jigo a kungiyar Kiristoci ta Najeriya ya rasu

News
Babban sakataren kungiyar kiristocin Najeriyar Musa AsakeHakkin mallakar hotoPREMUIM TIMES
Image captionMarigayi Rabaran Musa Asake ya yi fice wurin kare addinin Kirista da kuma matsayin Kiristoci

Babban sakataren kungiyar kiristoci ta Najeriya Rabaran Musa Asake ya mutu yana da shekara 67 a duniya.

Marigayin ya mutu ne da safiyar ranar Juma’a bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwar da Kakakin Majalisar Wakilai Hon. Yakubu Dogara ya fitar, ya nuna alhininsa ga iyalan marigayin da kuma kungiyar kiristoci ta kasar.

Dogara ya ce za a tuna da marigayin saboda rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Ya kara da cewa mutuwarsa “babbar rashi ne ga Kiristoci da kuma iyalansa”.

“Marigayin mutum ne mai son zaman lafiya tun lokacin da yake rike da mukamin babban sakataren cocin ECWA.”

“Mutum ne mai son ibada da kwazo kuma masanin addinin kirista ne,” in ji Dogara.

  • Yadda aka yi jana’izar Khalifa Isyaka Rabiu
  • Sai an ba coci kudi ake shiga aljannah- inji Fasto a Najeriya

Marigayi Musa Asake ya yi fice wurin kare addinin Kirista da kuma matsayin Kiristoci a Najeriya

A makon daya gabata ne marigayin ya nemi kiristoci su gudanar da zanga-zangar lumana a Najeriya domin yin kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen inganta tsaro a kasar musaman game da rikicin makiyaya da manoma.

Rabaran Musa Asake ya mutu ya bar mata daya da kuma yara.

Rahotanni sun ce kungiyar Kiristoci ta kasa za ta yi bayani nan bada jimawa ba a kan yadda za a binne marigayin.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.