Yadda aka cashe a bikin Sonam Kapoor

Sonam da angonta Anand AhujaHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionSonam da angonta Anand Ahuja

A ranar Lahadi 7 ga watan Mayun 2018, ne aka fara bikin ‘yar Sonam, inda aka yi sakun lalle wato ‘Mehindi’.

A wannan rana amarya da ango da iyayensu kai har ma da ‘yan uwa da abokan arziki an yi shigar kece raini, kuma da yawa daga cikin jaruman fina-finan Indiya sun halarci sakun lallan.

An yi wa amarya lalle mai kyau, haka kawayenta ma da sauran ‘yan uwanta mata duk an yi musu lallai, baya ga cashewa da aka yi a wajen, ga kuma kwalam da makulashe da aka ci a wajen.

Hoton sakun lallen Sonam KapoorHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionSonam Kapoor da angonta Anad Ahuja a ranar sakun lallenta

Iyayen Sonam, wato Anil Kapoor da Sunita Kapoor, baki har kunne tun da aka fara wannan biki, haka sauran ‘yan uwanta ma.

An dai yi shagalin bikin ne a gidan mahaifinta Anil Kapoor da ke Juhu a Mumbai.

Baban Amarya da dan uwan amarya wato Arjun Kapoor, sun cashe a wannan ranar sakun lallen, haka ita ma amarya ba a barta a baya ba, domin ta shiga fili duk da lallen da ke hannunta an cashe da ita.

A washegari kuma wato Talata 8 ga watan Mayun 2018, aka daura aure.

Manyan mutane baya ga jaruman fina-finan Indiya sun halarci wajen daura auren da ma bikin baki daya.

Amarya Sonam da angonta Anand AhujaHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionSonam Kapoor da angonta a ranar daurin aure suna dariya

Bayan daura aure kuma, daga bisani wato da yammacin ranar, an yi kasaitacciyar walima, inda kusan duk jaruman Indiya sun halarta.

Mahifin amarya, Anil Kapoor ya cashe sosai a wannan wajen walimar, domin rawar da ya yi, ango da amaryar ma ba su yi ba, saboda tsabar farin ciki.

Anil Kapoor ya yi rawa da mutane da dama a wajen walimar, kamar shi da Shahrukh Khan da Salma Khan da Ranveer Singh da Arjun Kapoor da Varun Dhawan da Karan Johar, sun fi kowa cashewa a wajen walima.

Sonam Kapoor da angonta a wajen walimaHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionSonam Kapoor da angonta a wajen walima
Wannan layi ne

Hotunan bikin Sonam Kapoor

Anil Kapoor da Shahrukh Khan da Salma Khan da amarya da ango suna cashewa a wajen walimaHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionAnil Kapoor da Shahrukh Khan da Salma Khan da amarya da ango suna cashewa a wajen walima
Arjun Kapoor da kannensa, Anshula da Jhanvi d akuma Khushi Kapoor a wajen bikin 'yar uwarsu Sonam KapoorHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionArjun Kapoor da kannensa, Anshula da Jhanvi d akuma Khushi Kapoor a wajen bikin ‘yar uwarsu Sonam Kapoor
Rani Mukherjee a wajen bikin Sonam KapoorHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionRani Mukherjee ma ta halarci bikin Sonam Kapoor
Varun Dhawan da budurwarsa Natasha Dalaal a wajen bikin Sonam KapoorHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionVarun Dhawan da budurwarsa Natasha Dalaal a wajen bikin Sonam Kapoor
Kanin mahaifin amarya Sanjay Kapoor da 'yar sa Shanaya da kuma wasu mahalarta bikin Sonam KapoorHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionKanin mahaifin amarya Sanjay Kapoor da ‘yar sa Shanaya da kuma wasu mahalarta bikin Sonam Kapoor
Abhishek Bachchan da matarsa Aishwarya da Salman Khan a wajen bikin Sonam KapoorHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionAbhishek Bachchan da matarsa Aishwarya da Salman Khan a wajen bikin Sonam Kapoor
Saif Ali Khan da matarsa Kareena Kapoor da 'yar uwarta Karishma Kapoor a wajen walimar Sonam KapoorHakkin mallakar hotoE TIMES
Image captionSaif Ali Khan da matarsa Kareena Kapoor da ‘yar uwarta Karishma Kapoor a wajen walimar Sonam Kapoor.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *