Kwankwasiyya ta gudanar da zaben shugabannin ‘APC’ a Kano

Politics
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne jagoran Kwankwasiyya
Image captionAna hasashen Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai nemi shugabancin kasar amma bai bayyana ba tukunna

Bangaren Kwankwasiyya na jam’iyyar APC ya gudanar da nasa zaben shugabanni a jihar Kano daban da wanda uwar jam’iyyar ta shirya.

Wannnan mataki ya kara fito da rikicin da ke tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mutumin da ya gada Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Bangaren na Kwankwasiyya ya ce ya samu fom din gudanar da zaben ne daga uwar jam’iyyar ta kasa kuma zai aika mata da sakamakon abin da ya wakana, kamar yadda shugaban tsagin Haruna Doguwa ya shaida wa Daily Trust.

Sai dai shugaban tawagar da APC ta tura domin gudanar da zaben, Chief John Halims, ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyar ba ta san da wani zabe ba banda wanda ya jagoranta.

Yunkurin da muka yi na jin ta bakin uwar jam’iyyar kan batun na Kano ya ci tura saboda jami’an da muka tuntuba ba su dauki wayoyinsu ba.

  • Zaben shugabannin APC ‘ya bar baya da kura’
  • Yaushe Kwankwaso da Ganduje za su shirya?

Jam’iyyar ta fada rikici ne a jihar Kano tun bayan da aka fara takun-saka tsakanin Ganduje da Kwankwaso sama da shekara biyu da ta gabata.

Duk yunkurin da aka yi na sasanta bangarorin biyu dai ya ci tura, kuma wannan tarukan da aka yi daban daban na nuna yadda rikicin yake kara kamari.

Ko da yake an gudanar da zaben sabbin shugabannin na APC a mazabu a wasu jihohi a ranar Asabar ba tare da an samu rikici ba.

A wasu wurare an bai wa hammata iska sannan an samu korafe-korafe da yawa.


Martanin APC

Game da sauran zabukan da aka ce an gudanar, APC ta ce ta yaba da yadda aka gudanar da zaben na shugabanninta a mazabu a sassan kasar.

A sanarwar da ta fitar, jam’iyyar ta amsa cewa an samu kura-kurai a wasu waurare inda ta ce ta kafa kwamitin sauraren koken wadanda suke ganin an saba masu.

A jihar Delta dai an kashe daya daga cikin ‘yan takarar zaben shugabannin jam’iyyar ta APC mai suna Jeremiah Oghoveta.

Rundunar ‘yan sandan jihar da ta tabbtar da faruwar lamarin, ta ce an daba ma sa wuka ne har ya mutu sakamakon takaddama da ta kaure tsakanin bangarorin jam’iyyar ta APC da ke hamayya a karamar hukumar Ughelli.

Wani bangare na jam’iyyar APC a jihar Bauchi kuma ya zargi bangaren gwamna Mohammed Abubakar da hana wa ‘yan takararsu fom domin takarar zaben.

A jihar Adamawa an dage gudanar da zaben na shugabannin APC a muzabu da ya kamata a gudanar a ranar Asabar.

Rahotanni sun ce an dage zaben ne zuwa Lahadi bayan wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun yi zargin cewa ‘yan takara da dama ba a ba su damar yankar fom na yin takarar zaben ba.

Me zai faru bayan tarukan jam’iyyar APC?

Adamawa na daya daga cikin jihohin da zaben shugabannin na APC zai iya haifar da rikicin siyasa musamman tsakanin manyan jiga-jiga jam’iyyar a jihar da suka hada da bangaren gwamna da Sanata Abdul’aziz Nyako da Nuhu Ribadu da kuma tsohon sakataren gwamnati Babachir David Lawal.

A jihar Zamfara ma an samu rikici a mazabar Sankalawa karamar hukumar Bungudu.

Wani mazaunin yankin, ya shaida wa BBC cewa sai da ‘yan sanda suka yi amfani da tiyagas bayan da matasa suka kama jifarsu.

Jihar na cikin jihohin da ke fama da rikicin jam’iyyar APC tsakanin bangaren Sanata Marafa mai wakiltar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattijai da kuma bangaren gwamna Abdul’aziz Yari.

Sannan rahotanni sun ce ‘yan sanda sun rufe hanyar shiga da fita Gusau babban birnin jihar saboda zaben shugabannin na APC a mazabu a ranar Asabar.

Wasu matafiya da lamarin ya rutsa da su, sun shaida wa BBC cewa sun shafe sama da sa’a biyar a wuri daya kafin jami’an tsaro suka bude hanyar shiga Gusau.

GusauHakkin mallakar hotoKABIRU JANGEBE
Image captionTun karfe 8 na safe aka rufe hanyar shiga Gusau har karfe 1 na rana

A jihar Rivers, rahotanni sun ce magoya bayan Sanata Magnus Abe sun yi zanga-zanga inda suka hana gudanar da zaben a wasu wurare a Fatakwal.

Bangaren Sanata Abe da ke neman takarar gwamna, sun yi korafi ne kan tsarin zaben tare da sukar shugabannin jam’iyyar musamman yadda aka bari sai a ranar zaben ‘yan takarar ke cike fom.

Wannan na zuwa a yayin da a jihar Ekiti aka dage babban zaben fitar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC bayan barkewar rikici.

Rahotanni sun ce wasu matasa sun abka wajen taron suka farfasa akwatunan zaben, tare da zubar da takardun kuri’un da aka kada.

‘Yan takara 33 ke neman kujerar gwamnan a APC da suka hada da tsohon gwamnan jihar Kayode Fayemi da kuma tsohon kakakin majalisar jihar Femi Bamisile.

A ranar 14 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben gwamnan na Ekiti, kuma APC na son kwace kujerar ne daga PDP da ke mulkin jihar.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa siyasa na ganin rigingimun da APC ke fama da su a jihohi na iya yi wa jam’iyyar illa sosai a zaben 2019.

Wasu ‘ya’yan jam’iyyar da suke ganin an saba ma su na iya ficewa zuwa wata jam’iyyar adawa.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *